Daukan aiki ba bisa ka'ida ba: Ma'aikatun tarayya 6 da majalisa za ta bincika

Daukan aiki ba bisa ka'ida ba: Ma'aikatun tarayya 6 da majalisa za ta bincika

Majalisar dattijaibta fara zargin saba ka'ida wajen daukan ma'aikata a wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Ma'aikatu da hukumonin da binciken majalisar zai shafa sun hada da; ma'aikatar tattara harajin tarayya (FIRS), jami'ar kowa da kowa (NOUN), hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya (FCSC), asibitin koyar wa na jami'ar Abuja, hukumar saka lantarki a karkara da rundunar sojojin ruwa.

Da yake gana wa da sauran mambobin kwamitin, Danjuma La'ah, shugaban kwamitin kula da daidaito a rabo da daukan sabbin ma'aiktan gwamnati, ya kwamitin da yake jagoranta ba zai yarda da rashinadalci wajen daukan sabbin ma'aikata ba a ma'aikatu da hukumomin tarayya.

"Na fadi cewa akwai bukatar mu gudanar da binciken kwa-kwaf domin tabbatar wa duniya cewa ba wata ma'aika muke yi wa bita da kulli ba. Za mu tabbatar da cewa kowanne yanki na Najeriya ya samu wakilci yayin daukan ma'aika a ma'aikatun tarayya domin samun hadin kai a kasa," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Tikar rawa da mace: Sheikh Daurawa ya magantu a kan bullar wani faifan bidiyo da ake zaton shine ke cashe wa

Ya ce kwamitin ba zai bata lokaci wajen dakatar da duk wata hukuma ko ma'aikatar gwamnati da ta saba wa dokar daidaito a daukan sabbin m'aikata ba tare da bayyana cewa ba zasu bari a kwari kowa ba yayin daukan aiki.

Wasu Sanatoci da ke zaman mambobi a kwamitinn sun yi korafn cewa hukumar kula da daidaito na boye wa kwamitin batun daukan sabbin ma'aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel