Da duminsa: Sojoji sun hallaka yan bindiga 58 a Zamfara

Da duminsa: Sojoji sun hallaka yan bindiga 58 a Zamfara

Akalla yan bindiga 58 sun rasa raukansu a hannun sojoji a jihar Zamfara yayinda Sojoji hudu suka rasa rayukansu kuma 4 sun jikkata a makon da ya gabata.

Hukumar sojin ta bayyana hakan ne da daren Asabar a shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita. Jawabin yace:

"A cigaba da dakile yan bindiga a jihar Zamfara, jami'an rundunar Operation HADARIN DAJI (OPHD) ta cigaba da samun gagarumin nasara kan yan bindigan da suka ki tuba."

"Za ku tuna cewa a ranar 3 ga Oktoba, 2019, yan bindiga sun afkawa jami'an sojin da aka tura 'Sunke' dake karamar hukumar Anka duk da tattaunawar sulhun da ake yi."

"Amma jaruman sojojin sun samu nasarar hallaka yan bindigan 19. Amma Sojoji 4 sun rasa rayukansu a harin."

"Sakamakon haka, dakarun sojin sun kaddamar da afkawa yan bindigan a ranar 6 ga Oktoba , 2019, da niyyar damke yan bindigan."

Sakamakon haka, a ranar 6 da 7 na watan Oktoba, 2019, a Bawa Daji, an kona gidaje a dajin Gubarawa da Bawa Daji yayinda Soji suka galabi yan bindigan kuma suka hallaka 39 wanda ya hada da wani hatsabibin kwamanda mai suna "Emir"."

Ga abubuwan da aka kwato daga hannun yan bindigan:

a. Bindigar AK47 guda 3

b.Harsashi 7.62mm guda 421

c.Harasahin PKT 30

d.Carbin harsasai 10

e.Babura 5

f. Shanaye 177

g.Wayoyin salula 7

h.Baturan waya 2

i.Wiwi

j. Layoyi

Sojoji hudu sun jikkata':"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel