Wani matashi ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa a Nasarawa

Wani matashi ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa a Nasarawa

Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke wani matashi mai sune Ahmed Abdullahi kan laifin dabawa matar mahaifinsa karfe har lahira.

Kakakin hukumar yan sanda, Ramhan Nansel, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai a ranar Asabar a garin Lafiyan Bare-bari.

Mitsa Nansel ya ce matashin ya aikata laifin ne misalin karfe 11 na daren Juma'a a Unguwar Yakubu, kauyen Agyaragu, karamar hukumar Obi na jihar.

A cewar kakain yan sanda, matashin ya arce bayan aikata laifin amma jami'ai suka bincikoshi da safiya Asabar.

Ya ce matashin na kokarin kashe mutane da dama a kauyen kafin jami'an yan sanda suka damkeshi.

Hukumar ta kaddamar da bincike kan dalilin da yasa ya aikata wannan laifi.

KU KARANTA: Malamin jami'a ya yiwa yarinyar yar shekara 13 fyade har lahira

A wani labarin daban, wani babban malami a kwalejin fasahar jihar Benuwe, Ugbokolo Andrew Ogbuja, ya gurfana gaban kotu a Makurdi kan laifin fyade yar shekara 13 mai suna, Ochanya Ogbanje, har ta mutu.

Wannan gurfanar ya faru ne shekara daya bayan mutuwar yarinyar a ranar 17 ga Oktoba, 2018 sakamakon fyaden da malamin jami'ar da dansa, Victor, sukayi mata.

Malamin ya gurfana ne gaban Alkali Ityonyiman kuma ya musanta zargin da ake yi masa yayinda aka karanta masa laifukan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel