An binciko yawan kudin da barayin Najeriya suka sata tun daga lokacin samun 'yancin kai zuwa yanzu

An binciko yawan kudin da barayin Najeriya suka sata tun daga lokacin samun 'yancin kai zuwa yanzu

- An yi kiyasin cewa an sace kimanin dala biliyan 582, kimanin naira tiriliyan 210 kenan a kudin Najeriya

- An sace wadannan kudin ne daga Najeriya tun daga lokacin da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960 zuwa yanzu

- Rahoton ya bayyana yadda Abacha ya tattare makudan kudade a kasar nan ya kai kasashen turai ya boye

An yi kiyasin cewa an sace sama da dalar Amurka biliyan dari biyar da tamanin da biyu ($582b), kimanin naira tiriliyan dari biyu da goma (N210tr) kenan a kudin Najeriya, daga shekarar 1960 lokacin da aka samu 'yancin kai zuwa yanzu.

An yi wannan kiyasin ne a wata jarida wacce aka yiwa taken 'Catch me if you can' ma'ana kama ni idan ka isa.

Cin hanci yana daya daga cikin babban kalubalen da Najeriya take fama da shi, inda aka bayyana cewa masu mulki sun karkatar da sama da naira tiriliyan 11 zuwa aljihunan su tun a shekarar 1999, yayin da kuma aka karkatar da sama da tiriliyan 1.3 na kudin al'umma daga shekarar 2011 zuwa 2015.

KU KARANTA: Hotuna: Jerin mata Musulmai guda 10 da suka fi kudi a duniya

Rahoton ya bayyana cewa kasar hukumar yaki da cin hanci ta kasar Birtaniya ta gano yadda aka cinye sama da dalar Amurka miliyan 117 a Najeriya tun daga shekarar 2006.

Jaridar ta bayyana cewa shugabannin Africa sun kware wajen boye kudaden da suka sata ta hanyar bude kamfani da asusun banki na karya su sanya kudin a ciki.

Haka kuma jaridar ta yi magana akan yadda tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya tattare kudi masu dumbin yawa ya boye a kasashen duniya, kuma babu wanda ya tambayi me yasa ya sata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel