KAEDCO: Namadi Sambo ya yi barazanar maka gidan jarida a kotu saboda yi masa kazafi

KAEDCO: Namadi Sambo ya yi barazanar maka gidan jarida a kotu saboda yi masa kazafi

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo ya ce 'tsantsagwaron karya ne da sharri' aka yi masa cikin wani labari da aka wallafa na cewa yana da hannun jari a kamfanin rabar da wutan lantarki na Najeriya, KAEDCO.

A sanarwar da aka fitar dauke da sa hannun tsohon mataimakin shugaban kasar, Mista Sambo ya ce; "An janyo hankali ne kan wani labari da aka wallafa a kafar yada labarai na intanet ta Daily Post ta wallafa kan wani bincike da ake yi kan kamfanin KAEDCO. Labarin ya yi ikirarin cewa nine na mallaki Kamfanin Rabar da Wutar Lantarki na Kaduna amma ta hannun wani."

Mista Sambo ya ce, "Ina son in fayyace cewa labarin karya ne kuma ba shi da tushe. An wallafa labarin ne domin a bata min suna. Hasali ma, bani da ko hannun jari guda a kamfanin ko wasu kamfanoni da aka sayarwa 'yan kasuwa lokacin ina kan mulki."

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

"A matsayina na shugaban kwamitin mayar da kamfanonin gwamnati hannun 'yan kasuwa, nayi ayyuka na kamar yadda doka ta tanada domin inganta kasar mu."

Sanarwar kuma ta ce Mista Sambo ya bukaci kafar yada labaran ta janye labarin sannan ta nemi afuwarsa cikin mako daya.

Mista Sambo ya ce, "Ina bukatar wadanda suka rubuta labarin da wadanda suka wallafa labarin su nem afuwa ta cikin mako daya."

Mista Sambo ya shawarci 'yan jarida su guji wallafa labaran karya da wadanda ba a tabbatar da su ba tare da hukunta wadanda suka ruwaito labaran karyar.

Ya shawarci 'yan jaridar su rika bin dokokin da ka'idojin aikin mai mutunci a kowane lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel