An gano mutumin da ya fito a bidiyon da ake zargin Sheikh Daurawa ne

An gano mutumin da ya fito a bidiyon da ake zargin Sheikh Daurawa ne

- Wani bidiyo da ya fara yawo a kafar sada zumunta ta zamani ya nuna wani mutumi da yake ta faman tikar rawa

- Sai dai wani abin mamaki da wannan bidiyo shine, wannan mutumi kamar su daya sak da shahararren malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano wato Sheikh Aminu Daurawa

- Wannan bidiyon dai ya kawo kace nace a shafukan sada zumunta, inda a jiya Shehin Malamin ya fito ya karyata wannan bidiyo

- To a yau ma an samu wani mutumi wanda ya fito ya tabbatar da cewa ba Sheikh Daurawa ba ne hasali ma wannan bidiyo an yi shi a can garin Maiduguri ne

Wani mutum mai suna Ibrahim Muhammad Jidda mazaunin garin Maiduguri ya bayyana cewa bidiyon nan da ake yadawa kan cewa Sheikh Aminu Daurawa ne ke tikar rawa a wurin taron biki ba gaskiya bane.

A cewar Ibrahim Muhammad Jidda cikin wani faifan sauti da ya saki a shafukan sada zumunta, a ala-hakika ba shi bane domin kuwa lamarin ya faru ne akan idon sa a wani dakin taro mai suna White Arena dake GRA a Maidugurin.

KU KARANTA: Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta akan zoben soyayya

‘Yace mutumin da aka nuno a cikin bidiyon kani ne ga wani dan siyasa a Maiduguri da ya samu halartar bikin, amma sam ba Mallam Daurawa bane sai dai sunyi kama sosai da Mallam Daurawa din.

Tun da farko dai an fara yada wannan bidiyo ne wanda ke nuna wani mutum da wata suna tikar rawa a wurin taron biki inda aka rika yada shi da sunan cewa wai Mallam Daurawa ne ke waccen rawar.

Sai dai tuni Shehin malamin ya fito ya karyata labarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel