Kasar Uganda ta sanya dokar kisa ga duk mutanen da aka kama suna luwadi

Kasar Uganda ta sanya dokar kisa ga duk mutanen da aka kama suna luwadi

- Majalisar kasar Uganda za ta sanya hannu akan wata doka da za ta bada damar yanke hukuncin kisa ga 'yan luwadi a kasar

- Dokar dai an so a sanyata a baya sai kuma aka dakatar, sai dai a wannan karon maganar ta taso da karfin ta

- An bayyana cewa mutane da yawa suna barin kasar sanadiyyar wannan doka da za a sanya a kasar

Wata doka da aka so sanyawa a kasar Uganda da za ta bada damar yanke hukuncin kisa kan 'yan luwadi a kasar yanzu haka gwamnatin kasar na kokarin dawo da ita cikin wannan makon.

Kasashen Afrika irin su Uganda suna daya daga cikin kasashe da suke da tsattsauran hukunci kan 'yan luwadi. Inda kasashe da yawa suke daukar luwadi a matsayin babban laifi, hakan ya sanya ake yankewa masu wannan halayyar hukuncin zaman gidan yari ko kuma kisa.

A farkon shekarar nan an fito da tsarin dokar da za ta bada damar yanke hukuncin kisa ga 'yan luwadi a kasar ta Uganda. Yanzu haka dai a wannan makon aka sake dauko maganar wannan doka inda za a sanya ta kafin karshen shekarar nan.

KU KARANTA: Ba nine na takura ta ba, ita ce da kanta ta bani lambarta sannan ta fara tura mini hotunan tsiraicin ta - Malamin Jami'a ya bayyana yadda lamarin yake

Ana tunanin cewar dokar za ta tabbata ganin cewa za a iya samun kaso biyu cikin uku na 'yan majalisar kasar su sanya hannu akan dokar.

'Yan luwadi da yawa sun bar kasar ta Uganda dalilin wannan doka da aka so sanyawa a shekarun baya, kuma yanzu haka wasu ma na kokarin barin kasar mutukar aka sanya wannan hukuncin.

An bayyana cewa a wannan shekrar an kashe 'yan luwadi guda uku da wani mata maza guda daya a kasar ta Uganda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel