Mota ta murkushe mahajjatan addinin Hindu 7 a gefen titi

Mota ta murkushe mahajjatan addinin Hindu 7 a gefen titi

- A ranar juma'a ne hukumar 'yan sanda ta tabbatar da murkushe mahajjatan addinin Hindu 7 da wani mai mota ya yi

- Mahajjatan da suka kunshi mata 4 da kananan yara 3, sun mutu nan take ne

- Titunan kasar Indiya na daga cikin tituna masu matukar hatsari a fadin duniya

A ranar Juma'a ne mota kirar bas ta murkushe mahajjata 7 da ke barci a gefen titi a arewacin Indiya.

Mahajjatan na kan hanyarsu ne ta zuwa tsarkakken kogin Ganges don yin wankan tsarki, in ji 'yan sanda.

Direban motar ya there amma ana cigaba da nemansa bayan da abin alhininin ya faru a jihar Uttar Pradesh, in ji kafofin yada labarai.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An hari jirgi bayan saukarsa a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas

Mamatan wadanda suka kunshi manyan mata 4 da kananan yarar uku na daga cikin maniyyatan da ke zuwa tsarkake kansu ne a kogin Ganges, wanda aka dauka a matsayin tsarkakken ruwa a addinin Hindu.

"Sun iso cikin dare ne. Mutane da yawa sun yanke shawarar barci a gefen titin kafin haske ya bayyana," in ji jami'in dan sanda Santosh Kumar Singh kamar yadda ya sanar da jaridar AFP.

"Da misalin karfe 4 na asuba, motar ta iso dauke da mahajjata. Akwai kwana a wajen kuma zai yuwu direban bai yi tsammanin akwai mutanen da ke barci ba gab da titin. Lokacin da yayi kwanar, ya bi ta kan mutane 7," in ji jami'in 'yan sandan.

Sama da mutane 150,000 ne a duk shekara ke rasa rayukansu a titinan kasar Indiya, wanda ake gani a cikin titina mafi hatsari a duniya.

Akan alakanta mace-macen ne da tsananin gudun masu ababen hawa, tituna marasa kyau da kuma tashin tabbatar da mutane sun bi doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel