'Yan daba sun kai wa shugaban NUJ na Kano hari

'Yan daba sun kai wa shugaban NUJ na Kano hari

Shugaban kungiyar 'yan jarida (NUJ) reshen jihar Kano, Ibrahim Shua'ibu ya sha da kyar a daren ranar Alhamis yayin da wasu 'yan daba suka kai masa farmaki da miyagun makamai.

Duk da cewa ba su yi masa rauni ba, sun kwace wa Shuiabu dukkan muhimman abubuwan da ya ke dauke da su da suka hada da kudi da wayarsa ta salula.

The Nation Online ta ruwaito cewa 'yan daban sun yi wa Shu'aibu barazana da wukake da wasu makamai masu hatsari kafin daga bisani suka amshe masa kayayyakinsa masu muhimmanci.

'Yan daban dai sun fara zama matsala da mazauna birnin Kano a cikin 'yan kwanakin nan.

Yana kan hanyarsa ta zuwa wurin duba lafiyarsa ne a Rijiyar Zaki a yayin da 'yan daban suka tare shi suka masa fashin.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Sanawar ta sakataren kungiyar, Kwamared Ibrahim Garba ya fitar ta ce Shu'aibu yana nan da ransa kuma cikin koshin lafiya amma ya rasa kayayyakinsa masu muhimmanci da suka hada da waya, kudi da wasu abubuwan.

Sanarwar ta kara da cewa wakilin 'yan jaridar na Kano ya bukaci Kwamishinan 'yan sanda ya dauki matakin gaggawa domin kawo karshe ayyukan da 'yan daba ke yi na hana mazauna garin samun kwanciyar hankali.

Ya ce, "Wurin da aka yi wa Ibrahim Garba fashi sanannen wuri ne saboda haka ya kamata 'yan sanda su dauki mataki cikin gaggawa na kama wadanda suka aikata harin tare da karbo masa wayansa da sauran kayayyakinsa masu muhimmanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel