Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar Alhamis ya zubar da hawaye a lokacin da ya ke korafi kan irin talauci da ke adabar al'umma a Najeriya.

A cewarsa, banbanci tsakanin masu kudi da talakawa ya yi yawa sosai kuma talakawan ne ke shan bakar wahala kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Basaraken ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke yin jawabi gaban wata kwamiti na Majalisar Dinkin Duniya kan cimma Maradun Karni (SDGs) a jihar Legas.

Ya zubar da hawaye a yayin da ya ke bayar da labarin yadda wani jariri ya mutu a hannun mahaifiyarsa a yayin da ta ke gab da samun taimako.

DUBA WANNAN: Mataimakin gwamna ya kama direbobi da dama masu saba dokokin tuki (Hotuna)

Sanusi ya shaidawa mahalarta taron cewa a ranar, mahaifiyar yaron ta shigo fada daga asibitin yara da ke kilomita 200 daga fadar.

A cewarsa, ya ji ihu mai karfi hakan ya sa ya tura wani ya dubo abinda ke faruwa amma sai mutumin ya dawo cike da hawaye a idonsa.

Sarkin ya ce jaririn ya mutu a hannun mahaifiyarsa yayin da ta ke kan layi tana jira a zo kanta domin ta roki kudin da za ta tafi asibiti a duba mata yaronta.

"Da na tambaya nawa ne kudin, sai aka ce min bai kai dallar Amurka buyar ba," a cewar Sarki Sanusi.

Ya kara da cewa, "irin wannan abubuwan suna faruwa a kullum a kasar. Yara suna mutuwa saboda iyayensu ba su da dallar Amurka biyar, mahaifiya tana kallo yaronta zai mutu saboda ba ta da dalla biyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel