Kyakkyawar budurwa da ta kamu da cutan dajin huhu (kansa) sakamakon shan 'Shisha' ta bada labarinta

Kyakkyawar budurwa da ta kamu da cutan dajin huhu (kansa) sakamakon shan 'Shisha' ta bada labarinta

Wata kyakkyawar yar kasar Amurka masu suna BeGracie a shafin Facebook ta bayyanawa duniya labarin yadda ta kamu da cutan dajin huhu sakamakon shan 'Shisha'.

BeGracie ta laburta yadda soyayyar da take yiwa Shisha yake kokarin hallakata yanzu kuma da alamun ba zata kai labari ba.

A cewarta: "Da na ce ba zan fadi halin da nike ciki ba amma na yi tunanin rayuwata za ta zama izina ga wasu."

"Wannan sakon ba na neman tausayi ko shahara bane, kawai ina son abokaina su sani hadarin da ke cikin shan Shisha."

"Shekarana hudu ina shan Shisha kullum. Idan ka san ni, na rantse za ka iya cewa babu inda zan je ba tare da Shisha na ba."

"Amma kash! Likitoci sun ce ina fama da ciwon huhu kuma huhu na ya kamu da sani. An tabbatar da cewa shan Shisha ne ya janyo min cutan."

Watanni na bakwai yanzu ina fama da (tari, amai, gaza numfashi da zazzabi) kuma ina ta boyewa amma hakan na lalata huhuna. Amma babu komai, ina fatan hakan ba zai faru da wani ba."

KU KARANTA: Yadda wani matashin Arewa ya zama matukin jirgi bayan shekaru 24 yana mai sharan filin jirgi

A farkon makon nan, Legit.ng Hausa ta kawo rahoton cewa Sinadaran karfe da kan janyo cutar daji da aka fi sani da kansa na kunshe da yawan gaske cikin kayan shakatawa na 'Shisha' da Medwakh fiye da sigari, sabon binciken kasar UAE ya bayyana.

Malaman kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun samu cewa idan aka hada hadarin Shisha da Sigari, sinadaran nickel, chromium, copper da zinc masu cutarwa sun fi yawa cikin Shisha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel