Mahakurci mawadaci: Yadda wani matashin Arewa ya zama matukin jirgi bayan shekaru 24 yana mai sharan filin jirgi

Mahakurci mawadaci: Yadda wani matashin Arewa ya zama matukin jirgi bayan shekaru 24 yana mai sharan filin jirgi

Muhammad Abubakar ya fara aiki ne shekaru 24 da suka shude matsayin mai shara a filin jirgin sama. Wannan bai shine manufarsa ba amma abubuwa sun gagara.

Gabanin fara aikin shara da goge-goge, ya nemi shiga kwalejin fasahar Kadpoly dake jihar Kaduna amma ba'a karbeshi ba. Kawai sai ya fara aikin shara a kamfanin jirgin saman Kabo Air.

A lokacin N200 a ke biyansa a rana. Amma Abubakar ya hakura kuma ya jajirce har ake daukesa matsayin karamin ma'aikaci a kamfanin jirgin dake Maiduguri.

Daga nan, sai ya nemi aikin ma'aikatan cikin jirgi a kamfanin, da suka irin namijin kokarin da yayi, sun bashi aikin.

Bayan shekaru takwas yana aikin kan albashi N17,000 a wata, sai ya koma kamfanin jirgin saman Aero Contractors matsayin mai tarban matafiya.

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa da ta kamu da cutan dajin huhu (kansa) sakamakon shan 'Shisha' ta bada labarinta

Bayan lura da hazakarsa da wani mataimakin manajan Aero yayi, sai aka kara masa kudin albashi zuwa N170,0000. Da farko da aka biyashi bai yarda nashi bane, yayi kokarin mayar da kudin.

Maimakon tunain facaka da kudin albashinsa, Abubakar ya rika adashi. Sai ya garzaya wajen diraktan inda ya bayyana masa niyyar san zama matukin jirgi, sai aka bashi daman zuwa horon tukin jirgi a kasar Canada.

Da ya dawo Najeriya, sai ya bukaci wani takardan tukin jirgin kasuwa kuma kamfanin suka kara bashi daman komawa Canada kara ilimi kuma ya kammala.

Bayan shekaru takwas yana aiki a Aero Contractors, Muhammad Abubakar ya zama Kyaftan a kamfanin jirgin Azman Air.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel