Wani malamin jami'a yace bidiyon fallassar da BBC ta yi kirkirarre ne

Wani malamin jami'a yace bidiyon fallassar da BBC ta yi kirkirarre ne

- Wani malamin jami'ar Najeriya dake Nsukka yace bidiyon fallasar da BBC tayi akan malami masu neman dalibai mata don lalata, kirkirarre ne

- Malamin, wanda kuma fasto ne yace idan an lura da kyau za a gane cewa yarinyar ce taje har ofishin malamin tare da jan hankalinsa

- Faston, ya kara da jawo hankulan maza akan irin wannan lamurran domin kwa a cewarsa, mata kan ja hankulan maza sannan daga baya su yi ikirarin an ci zarafinsu

Wani malamin jami'ar Najeriya da ke Nsukka kuma fasto mai suna Joseph Nnaemeka Chukwuma ya zargi cewa bidiyon tonon asirin da BBC tayi na malaman jami'o'i masu neman dalibansu da lalata kirkirarre ne.

Malamin jami'ar wanda kuma fasto ne, ya ja kunne maza da su kiyaye, domin kuwa wasu matan kan je ddon daukar hankulansu daga baya kuma su zargesu da cin zarafinsu.

KU KARANTA: Wasu mabiya sun ja shugaba a kasa akan rashin cika alkawari

Malamin jami'ar ya kara da cewa, idan aka dubai bidiyon da idon basira don tantancewa, za a gano cewa, "Yarinyar ta je ne don jan ra'ayin malamin jami'ar har ofishinsa inda daga baya aka yi kare-kare akai".

Idan zamu tuna dai a ranar litinin ne BBC ta saki bidiyon binciken sirrin da 'yar jarida Kiki Mordi tayi a wasu jami'o'in Najeriya da kasar Ghana akan malaman manyan makarantun masu lalata da dalibai mata akan maki.

Tuni kuwa jami'ar jihar Legas ta dakatar da malamanta biyu da ta hango a bidiyon don ta samu damar bincikar lamarin.

A jiya kuma hukumar jami'ar ta kafa kwamitin bincikar badalar tare da sauraron koken daliban jami'ar da malaman akan lamarin.

Idan bazaku manta ba, a kwanakin baya jami'ar Ahmadu bello da ke Zaria ta kori wasu malamanta akan irin wannan muguwar dabi'ar ta neman dalibai mata don lalata dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel