GITEX: 'Dan Najeriya ya zama zakara a gasar sabbin kirkire-kirkiren fasahar sadarwa

GITEX: 'Dan Najeriya ya zama zakara a gasar sabbin kirkire-kirkiren fasahar sadarwa

Wani dan Najeriya, Abdulhakim Bashir a ranar Laraba a birnin Dubai na kasar Tarayya Larabawa ya zama zakara a gasar ilimin na'ura na wucin gadi (Artificial Intelligence) a wurin taron baje koli na fasaha ta GITEX da ake gudanarwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Cibiyar kasuwanci ta Dubai ce shirya gasar na sabbin kamfanoni domin koyar da tunani da kirkire-kirkire ga matasa da ke shirin kafa kamfanoni.

Manhajar da Bashir ya kirkira mai suna 'Chiniki Guard' an yi ta ne domin hana sata a shaguna da gidajen al'umma.

A zantawar da manema labarai suka yi da Bashir a Dubai, ya ce: "Chiniki Guard yana bayar da cikakken bayanin abubuwan da suka wakana a kanti/shago kai tsaye. Yana kuma bayar da sanarwa idan anyi sata ta hanyar yin nazarin faifan bidiyo da CCTV ta nada."

DUBA WANNAN: Rigingimu: Mambobin PDP sun fice daga zauren majalisar dokokin jihar Filato

Bashir ya ce manhajar za ta kare kashi 80 cikin 100 na shaguna da kantunna daga fadawa cikin matsalar rashin kudi sakamakon satar da ma'aikatansu ko masu sayaya ke yi.

Ya ce, "munyi tunanin yadda za muyi amfani da ilimin na'ura na wucin gadi domin kawo karshen wannan matsalar mu kare mai shago daga asara. Ciniki Guard na da bangarori uku da suka hada da manhajar nadan faifan bidiyo, manhajar waya da fuskar wallafa bayanai."

Matashin dan Najeriya ya samu kyautan $10,000 saboda zama zakara a sashin ilimin na'ura na wucin gadi.

Shugaban sashin kula da sabbin kirkire-kirkire na Najeriya a wurin gasar, Dakta Amina Sambo ta ce nasarar Bashir ya tabbatar da cea matasan Najeriya suna da basira a fanin fasahar sadarwa.

Ta kuma ce ofishinta zai cigaba da bawa sauran 'yan Najeriya tallafi a bangaren na fasahar sadarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel