An bawa malaman Islamiyya 6 masauki a gidan gyaran hali a Kaduna

An bawa malaman Islamiyya 6 masauki a gidan gyaran hali a Kaduna

Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Litinin ta bayar da umurnin tsare malaman islamiyyan Ahmad Bn Hambal da 'yan sanda suka kama a wani gidan gyaran tarbiya.

'Yan sandan sun kai sumame makarantar a ranar 27 ga watan Satumba a Rigasa Kaduna inda suke gano dalibai fiye da 300 da aka yi ikirarin cewa ana cin zarafinsu tare da keta hakkinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa nn gurfanar da malaman shida ne a gaban alkalin kotun, Musa Lawaal Mohammed na kotu ta 16.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi babban rashin wani jigon ta

Malaman da aka gurfanar sun hada da Ismail Abubakar, Umar Abubakar, Abdul’azeez Adam, Abubakar Muktar, Abdullahi Auwal and Salisu Ibrahim.

Dan sanda mai shigar da kara Hassan Malan ya shaidawa kotu cewa ana tuhumar mutane shidan da laifin hadin baki, tsare mutane ba bisa ka'ida ba, zalunci da saduwa ba ta hanyar da ta dace ba.

Mai shigar da karar ya kuma ce har yanzu 'yan sandan na cigaba da bincike.

Lauya mai kare wadanda ake zargin, Sani Shehu Surajo ya shaidawa kotu cewa sun zo kotun ne kawai saboda sun san abinda ke faruwa amma kotun ba ta da ikon sauraron shari'ar.

Ya kuma roki a bari wadanda ake zargin su cigaba da zama a hannun 'yan sanda tunda ba a kammala bincike kan zargin da ake musu ba amma mai shigar da kara ya ce 'yan sanda ba su da wurin da za su cigaba da ajiye su.

A bangarensa, alkalin kotun ya ce kotun ba ta ikon sauraron shari'ar saboda daya daga cikinsu ana tuhumarsa da babban laifi ne wadda sai babban kotu ne ke da hurumin sauraron shari'arsa.

Hakan yasa ya bayar da umurnin a ajiye wadanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kaduna kuma ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel