Dukan mace a shagon sayen kayan batsa: Kwamitin da aka kafa a kan Sanata Abbo ya mika rahotonsa

Dukan mace a shagon sayen kayan batsa: Kwamitin da aka kafa a kan Sanata Abbo ya mika rahotonsa

Kwamitin wucin gadi da majalisar dattijai ta kafa domin binciken zargin mamba a majalisar, Sanata Elisha Abbo, ya mika rahotonsa a gaban majalisar ranar Talata.

Abbo, sanata mai wakiltar mazabar jihar Adamawa ta Arewa, na fuskantar tuhuma a kan dukan wata mata a wani shagon sayar da kayan batsa.

Shugaban kwamitin, Sam Egwu (dan jam'iyyar PDP, ne ya gabatar da rahoton kwamitin yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A ranar 3 ga watan Yuli ne majalisar dattijai ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki Sanata Abbo bisa zarginsa da sharara wa wata mata mari a wani shagon sayar da kayan batsa da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Manyan ma'aikatu 10 da Buhari ya ware wa makudan biliyoyi a kasafin 2020

An ga dan majalisar a cikin wani takaitaccen faifan bidiyo yana marin matar bayan wata cacar baki ta shiga tsakaninsu.

Sanata Abbo ya mammari matar ne saboda ta goyi bayan matar dake jiran shagon yayin da wani sabani ya shiga tsakaninsu.

Lamarin ya faru ne ranar 11 ga watan Mayu, 2019, ana saura wata guda a rantsar da Abbo a matsayin Sanata mafi karancin shekaru a cikin sanatocin da aka zaba a zaben shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel