An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)

An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)

Wata tawagar jami'an tsaro na hadin gwiwa ta Rundunar 'yan sandan jihar Borno da jami'an Operation Puff Ader sun yi nasarar kama wasu manyan wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi 17 a jihar.

Yayin baje kolinsu ga masu manema labarau, 'yan sandan sun bayyana abubuwan da suka kwato daga mutanen da suka hada da; ganye da ake zargin wiwi ne, s*ck and die, kwayan Drazzapan da tukunyan shan Shisha.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Ndatsu ya ce, "Kana iya ganin abubuwan da muka kwato, busasun ganyayyaki da ake zargin wiwi ne, s*ck and die mai yawa, kwayar Drazzapan, tukunyar shan Shisha da ake amfani dashi wurin busar ganyayakin da ake badda kama da su kamar ganyen Shisha."

An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Pantami da shugaban NITDA sun kirkiri wata muhimmiyar na'ura

An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
Asali: Twitter

An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
An kama wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Borno (Hotuna)
Asali: Twitter

Yan sandan kuma sunyi baje kolin wasu 'yan damfara da aka kama. An same su da takardun daukan aiki na bogi na NNPC, NPS da sauran hukumomin gwamnati da suke amfani da shi wurin cutar al'umma su karbe musu makuden kudi da sunan za su samar musu da aiki.

Shugaban 'yan sandan ya ce, "Mun kama 'yan damfara da suke kware wurin buga takardan daukan aiki na bogi bayan sun karbi makuden kudi daga hannun al'umma. An sami wasu daga cikinsu da takardan daukan aiki na bogi na NIPOST da NNPC. Wadanda aka kama sun hada da Gideon Ndanga (32) da Francis Josiah daga jihar Borno."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel