HOTO: Yau wace rana! Dino Melaye ya sarawa Buhari

HOTO: Yau wace rana! Dino Melaye ya sarawa Buhari

Kai ne wanda yayi min ihu bara ko? A'a Baba ayi min afuwa? Wai shine me Dino Melaye da Buhari ke tattaunawa?

HOTO: Yau wace rana! Dino Melaye ya sarawa Buhari
HOTO: Yau wace rana! Dino Melaye ya sarawa Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kiyasin da aka gina kasafin kudin 2020 a kai da hotunan taron

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye, na daya daga cikin wadanda suka jeru domin jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari yayinda ya kammala gabatar da kasafin kudin 2020 ga majalisar.

Duk da cewa bamu sani hakikanin abinda yake fadawa Buhari ba, yadda Dino Melaye ya sarawa Buhari ya nuna cewa yana jinjina masa ne, bayan ya yi masa ihun bamaso a shekarar 2018 da ya zo gabatar da kasafin kudi.

Melaye ya fara samun matsala da Buhari ne lokacin da rikici ya barke cikin jam'iyyar APC a 2018.

Zuwa karshen wa'adinsa na farko, Dino Melaye ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

A cikin wadanda suka yiwa Buhari adawa da ihu a bara, shi kadai ya samu daman dawowa majalisa a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel