Na yi ne saboda kada abin ya shafi talaka - Jerin kayan abinci 22 da Buhari ya togaciyewa haraji
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar kasafin kudin 2020 ga majalisar dokokin tarayya domin su duba kuma su tabbatar da shi domin aiwatarwa.
A wannan karon, Buhari ya hada da wani doka na karin kudin harajin kayayyaki.
A cewarsa, wannan sabuwar doka na haraji za ta kara kudin harajin kayayyai daga 5% zuwa 7.5%.
Amma ya bayyana cewa akwai wasu kayayyakin masarufi 21 da ya togaciye kuma wannan haraji ba zai shafesu ba.
KU KARANTA: HOTO: Yau wace rana! Dino Melaye ya sarawa Buhari
Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin wadannan kaya:
1. Kayayyakin karatu
2.Biredi
3.Masara
4. Shinkafa
5. Alkama
6. Gero
7. Sha'eer
8. Sorghum
9. Kifi
10. Flawa
11. Kayan itace
12. Kayan miya
13. Doya
14. Gwaza
15. Dankalin turawa
16. Dankalin Hausa
17. Gyada
18. Kwai
19. Nama (Kowani iri)
20. Gishiri
21. Kayan maganin gargajiya
22. Ruwan sha
Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi hakan ne domin sauke nauyin kan talakawa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng