Hotunan bikin wata kyakyawar gurguwa da angonta sun jawo cece-kuce a arewa

Hotunan bikin wata kyakyawar gurguwa da angonta sun jawo cece-kuce a arewa

- A cikin makon da ya gabata ne hotunan wata tsaleliyar gurguwa da mijinta suka cika shafukan sada zumunta, abinda ya jawo cece-kuce a wajen samari da 'yam mata

- Ba komai yafi baiwa mutane mamaki ba illa ganin angon garas lafiyayye dta kuma tsantsar kaunar da ya dinga nunawa amaryarsa

- Amarya Bilkisu dai a tarihinta da jaridar Legit.ng ta bibiya ta gano cewa hatsarin mota ne ya maida ita hakan

A makon da ya gabata ne shafukan sada zumunta suka cika fal da hotuna tare da bidiyoyi na wata kyakyawar budurwa akan keken guragu da kyakyawan angonta. Abinda ya jawo cece-kuce a wajen samari da 'yam mata.

Mutane da yawa sun yi ta saka hotunan da bidiyon ne sakamakon birgesu da amarya da angon suka yi. Angon ya nuna matukar kaunar da yake wa amaryarsa duk da kuwa tana da nakasa. Ita kuwa amaryar ta nuna cewa nakasa fa ba tawaya bace.

KU KARANTA: Kukah ya bayyana dalilin da yasa ake yiwa sarki Sanusi II bita da kulli

A bibiyar shafin Bilkisu na Instagram da Legit.ng tayi, ta gano cewa, amarya Bilkisu na da shekaru 23 a duniya.

Ba da wannan nakasar kuma aka haifeta ba. Don kuwa ta bayyana cewa tana da shekaru 15 kacal a duniya hatsari ya ritsa da ita inda ta samu rauni a kashin bayanta.

Matsalar da ta shafi aiki ko amfani da kafafunta.

Farfadowa kuwa daga wannan matsalar sai a sannu. A don haka ne sai da Bilkisu ta koyi abubuwa da yawa.

Hakan kuwa bai sa Bilkisu ta fidda rai daga cikar burinta ba.

A shekarar 2018, Bilkisu ta samu gurbin karatun jarida a jami'a.

Ga abinda ta wallafa a shafinta: "Ga wadanda basu san labarina ba, gashi a takaice. Shekaru 8 da suka gabata na samu hatsari inda na raunata kashin bayana. Lokacin inada shekaru 15. Raunin yasa bana iya amfani da kafafuna. Komai kuwa ya tsaya min,"

Ta kara da cewa, "Na koma kamar jaririya. Sai da na koyi abubuwa da yawa. Waraka daga cutar da na hadu da ita sai a sannu. A 2017, na nemi gurbin karatu a jami'a amma ban samu ba. A 2018 na kara nema inda na samu. Dukkan godiya na ga Allah. Bayan samun gurbin karatun kuma aka dauki nauyina."

A ranar asabar da ta gabata ne aka daurawa Bilkisu aure da masoyinta Adnan.

Muna musu fatan alkhairi da kuma fatan amarya Bilkisu zata zamo madubin dubawa ga masu nakasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel