Fushin naki aminta da soyayyarsa ta sa ya watsa min acid a fuska, in ji Rangoli

Fushin naki aminta da soyayyarsa ta sa ya watsa min acid a fuska, in ji Rangoli

- Rangoli Ranaut, 'yar uwar Kangana Ranaut, jarumar Bollywood ta bayyana yadda saurayin da ta ki amsar tayin soyayyarsa ya watsa mata guba

- Ta yi bayanin yadda ta dau shekaru 5 a asibiti tana fama inda akai mata aiki har kashi 54

- Ta kara da nuna yadda hakan ya dakatar da lamurran rayuwarta tare da sauya mata halittarta

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, Rangoli Ranaut, 'yar uwar Kangana Ranaut, jarumar Bollywood ta bayyana yadda ta warke bayan mummunan lamarin da ya faru da ita.

Ta bayyana cewa saurayin da ta ki karbar tayi soyayyarsa ne ya fusata. Hakan kuwa yasa ya watsa mata lita daya na acid a fuska don nakasata.

KU KARANTA: Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya

Ta kara da cewa, sai da aka yi mata aiki kashi 54 a fuskar kafin a samu ta dawo daidai. Duk da haka kuwa, kunnenta guda daya bai koma yadda yake ba sakamakon barnar da gubar tayi mata.

"Mutane da yawa sun tausaya min rasa kyau na da nayi. Amma kuma babban tashin hankali shine kana kallo sassan jikinka na narkewa, ina tunanin kyau shi ne abu na karshe da zaka iya tunawa,"

"Bayan shekaru 5 tare da aiki 54, likitoci basu iya gyara min kunnena ba. Na rasa ido daya, sai da aka yi min aiki akansa. Likitoci sun yanko naman jikina don gyara nono na daya da ya samu matsala. Yayin shayarda yarona, na sha wuya," Rangoli ta wallafa a shafinta na tuwita.

Ta kara da cewa, "Ko a yanzu bana iya mikar da wuyana. Wani lokacin kaikayi kadai kansa in yi burin mutuwa. Ni ce kan gaba a ajinmu lokacin ina jami'a, amma dole na hakura na yi shekaru 5 a asibiti,"

A karshe, Rangoli ta nuna yadda dangi da abokan arziki suka zame mata ginshiki a rayuwarta yayin wannan jarabawar.

"Ban san me zance ba. Mijina a yanzu, wanda a da abokina ne yayi kokari. Shi ke wanke min ciwuka na ya kuma tsaya yana jira a fito dani daga tiyata. Yayi kokari na shekaru. 'Yan uwana da iyayena kuwa sun zama jigon kwarin guiwata. Ba zan iya saka musu ba." in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel