Ajali ya yi kira: Ruwa ta cinye mutum 38 a Bauchi

Ajali ya yi kira: Ruwa ta cinye mutum 38 a Bauchi

- Manoma 38 sun mutu a hanyarsu ta zuwa gona a karamar hukumar Kirfi na jihar Bauchi

- Rahotanni sun nuna cewa jirgin ruwan da suke ciki ya kife ne inda ruwa ya halaka 38 cikinsu sai mutum biyu kawai suka tsira

- Shugaban karamar hukumar Kirfi, Bappa Danmalikin Bara ya ce an nemi taimakon masu ninkaya na gargajiya amma ba ayi nasarar ceto su ba

Mutane 38 ne suka mutu sakamakon ruwa da ya cinye su a rafin Kirfi da ke karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban karamar hukumar Kirfi, Alhaji Bappa Danmalikin Bara, yayin zantawa da ya yi da manema labarai a jiya ya ce, "Ina son in mika ta'aziyya ta ga al'ummar Kirfi, jihar Bauchi da Najeriya baki daya kan rashin 'yan uwan mu da mu kayi a hanyarsu ta zuwa gona.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

"Sun shiga kwalekwale; su 40 ne a cikin kwalekwalen amma 38 da cikinsu sun nutse cikin ruwan mutum biyu ne kadai suka tsira.

"Mun gano gawarwaki biyu a garin Badara kuma mun tuntubi masu ceto mutane na gargajiya amma ba muyi nasarar ceto su ba. Muna tsamanin dukkansu sun mutu. Muna fatan Allah ya jikansu da rahama ya kuma yafe musu kurakurensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel