Malamin jami'an Legas da aka kama a bidiyon 'Zina don bayar da maki' ya yi magana

Malamin jami'an Legas da aka kama a bidiyon 'Zina don bayar da maki' ya yi magana

Wani malami a jami'ar Legas (UNILAG), Boniface Igbeneghu da aka kama a faifan bidiyo yana neman yin lalata da wata 'mai neman shiga jami'ar' ya sha alwashin cewa ba zai yi tsokaci a kan lamarin ba duk da matsin lamba da al'umma ke yi.

A hirar da ya yi da Punch, malamin jami'an da aka dauka a faifan bidiyo yana cin zarafin wata 'yar jaridan BBC da tayi badda kama a matsayin mai neman shiga jami'a ya ce yin tsokaci kan lamarin saba dokar UNILAG ne.

A cikin wani bangare na faifan bidiyon, Igbeneghu ya shaidawa Kiki Mordi, 'yar jaridar da tayi badda kama yadda wasu malaman jami'an ke zina da dalibai sannan su tura su wurin wasu malaman.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Ya gayyaci ta zuwa ofishinsa na dan wasu lokuta domin koyar ta ita wasu darrusa kafin daga baya ya fara mata hirar da ba u dace ba masu alaka da zina.

Cocin Foursqure inda malamin ke aiki a matsayin fasto sun dakatar da shi yayin da mahukunta UNILAG suma suka bukaci ya koma gefe guda har zuwa lokacin da suka kammala bincike.

Punch ta jiyo malamin yana cewa, "Jami'ar Legas na ke yi wa aiki; Idan kuna son wani martani, kuyi magana da jami'an.

"Ku tuntubi sashin hulda da jama'a za su fada muku halin da ake ciki. Idan nayi magana, zan saba dokar jami'a. Ku dena matsa min har sai na fadi wani abu bayan abinda na fadi yanzu."

Wani malami daga jami'ar kasar Ghana da shima aka kama shi bidiyon ya yi martani a baya inda ya ce zai maka BBC a kotu a ranar Talata kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel