Amarya ta kama ango yana lalata da daya daga cikin kawayenta amma bata fasa aurensa ba

Amarya ta kama ango yana lalata da daya daga cikin kawayenta amma bata fasa aurensa ba

Wata amarya ta kama angonta yana cin zarafin daya daga cikin kawayenta kwanaki biyu gabanin aurensu amma duk da hakan ta amince da aure shi amma a yanzu ana tuhumarsa da laifin yin lalata da karfi da yaji kamar yadda Linda Ikeji Blog ya wallafa.

Ana tuhumar Daniel Carney dan shekaru 28 a duniya da 'saduwa da matar da ba ta cikin hayyacinta.' An ce ya yi lalata da wata kawar amaryar a wurin liyafa da aka shirya gabanin auren a otel din Shawnee a Smithfield, Pennsylvania a cewar 'yan sanda.

Karar da aka shigar a kotu ya ce kawar amaryar da shaidawa masu bincike cewa ita da kawayenta da 'yan uwanta sune shan giya ne kusa da rafin Delaware don murnar daurin auren da za ayi a ranar 1 ga watan Satumba.

Masu bincike sun ce kawar amaryar ta bugu sosai yayin da ta ke rafin hakan yasa amaryar ta umurci Carney ta taimaka ya mayar da kawar nata zuwa inda ake ajiye motocci a gaban otel din.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Wacce abin ya faru da ita ta ce ta tuna lokacin da aka kama hannunta daga rafin amma sai ta farka ta ga Carney yana cizon ta kuma yana jan ta zuwa dakin canja kaya na maza da ke otel din a cewar Pittsburgh Post-Gazette.

Ta ce hankalinta ya sake gushewa kuma daga baya ta farka ta ga Carney yana shafa jikinta a dakin canja kayan na maza. Ta kara da cewa ta ga an tube mata 'yan kamfan ta.

Yayin da abin ke faruwa, kawar amaryar ta ce amaryar ta shigo dakin. Ta kara da cewa za ta iya tunawa cewa taji amaryar na yi wa Carney fada. 'Yan sanda sun ce daga bisani masoyyan sun fito waje suna ta musayar kalmomi.

Acewar wanda abin ya faru da ita, "Rikici ake ta tafkawa a wurin liyafar auren" daga daren ranar har zuwa safe.

A safiyar ranar da za a daura auren, Carney ta aike wa matar sakon tes ya nemi afuwarta, inda ya nemi a manta da abinda ya faru domin su cigaba da rayuwa cikin farin ciki. Ya kume bukaci ta sha maganin hana daukan ciki na gaggawa inji 'yan sandan.

Wani abokin Carney ya shaidawa WNEP cewa an daura auren masoyan duk da zargin da ake yi masa ne yin lalata da kawarta.

Ana zargin Carney da laifin zina da wacce ba ta cikin hayyacinta, da karamin laifi na cin zarafi da kuma wani karamin laifi na barazanar yi wa wani rauni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel