Zaben gwamna: 'Yan jam'iyyar APC 6,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Bayelsa

Zaben gwamna: 'Yan jam'iyyar APC 6,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Bayelsa

- Gabanin zaben gwamna na jihar Ekiti, a kalla magoya bayan jam'iyyar APC 6,000 sun fice sun koma jam'iyyar PDP

- A yayin karbar wadanda suka shigo jam'iyyar ta PDP, Gwamna Seriake Dickson ya bukaci al'ummar jihar su juya wa APC baya kamar yadda suka yi mata a 2015

- Gwamnan ya ce wanda zai gaje shi zai dora daga inda ya tsaya idan ya yi nasarar lashe zabe

A kalla mambobi da magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bayelsa gabanin zaben gwamna da za ayi a jihar.

A yayin da ya ke maraba da sabbin 'yan jam'iyyar ta PDP, Daily Sun ta ruwaito cewa Gwamna Seriake Dickson ya bugi kirjin cewa jam'iyyar APC ba za ta lashe ko mazaba guda ba a zaben da a gudanar a watan Nuwamba duk da cewa ita ke mulkin kasa.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Gwamnan ya fadawa APC ta shirya shan kaye duk da barazana da kisa da ta ke yi wa 'yan Bayelsa.

Ya bayyana cewa ya yi imanin al'ummar jihar za su juya wa APC da dan takararta baya kamar yadda su kayi musu a shekarar 2015.

Ya shaida wa taron mutanen cewa, "Muna gabatar muku da tikiti mai tabbas, tikitin cigaba ba tikitin da zai mayar da jihar nan matattaran 'yan daba da masu laifi ba inda mutanen mu za su rika guduwa kamar yadda suke yi a baya.

"Shi yasa muke gabatar muku da wannan tikicin ta ikon Allah gwamnan ku a 220 shine Sanata Douye Diri.

"Kamar yadda muka kayar da su a 2015 duk da daurin gindin da suke dashi daga gwamnatin tarayya, za mu sake kayar da su wannan karon ma tazarar za ta fi na baya a watan Nuwamba."

Legit.ng ta kawo muku cewa karamin ministan man fetur, Timipre Silcer ya ce zai yi amfani da matsayina domin kawo cigaba a jihar a maimakon amfani da karfin gwamnatin tarayya domin kawo tashin hankali a zaben na ranar 16 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel