Lalata da dalibai don basu maki: Cocin Foursquare ta dakatar da malamin jami'a

Lalata da dalibai don basu maki: Cocin Foursquare ta dakatar da malamin jami'a

Kamar yadda muka sani lamarin cin mutuncin dalibai mata ya zama ruwan dare a jami’o’i Najeiya ta yadda lakcarori da dama ke neman lalata dasu ko kuma su muzantawa rayuwarsu a makarantun idan har suka ki basu hadin kai.

A kwanan nan ne labarin wani babban lakcaa a jami’ar UNILAG kuma fasto cocin Foursquare Gospel Church, Dr. Boniface Igbeneghu, ya karade shafukan zumunta bayan an kama shi a cikin wani faifai bidiyo yana kokarin neman hadin kan wata yar jarida da tayi basaja a matsayin yar shekara 17 da ke neman shiga makarantar.

A bidiyon wanda ya karade shafukan sadarwa, an gano faston kuma babban lakcaran yana zantukan da basu dace ba da matashiyar inda harma ya nemi ta kashe fitila sannan ta sumbace shi na minti guda.

Lakcaran ya kuma tambayi matashiyar game da rayuwar jima’inta jim kadan bayan yayi mata addu’a kan ta mika rayuwata ga Yesu. Ya kuma bukaci ta matso da kujerarta kusa dashi domin sumbatar shi.

Don haka a yanzu cocin ocin The Foursquare Gospel Church ta nesanta kanta da Dakta Boniface Igbeneghu.

Cocin ta sanar a shafinta na Twitter cewa: "Shugabancin wannan coci ya samu labarin abin da aka nuna Dakta Boniface yana aikatawa a bidiyon binciken BBC Africa Eye.

KU KARANTA KUMA: Sulhu da yan ta’adda ba zai taba magance matsalolin tsaro ba – Tsohon Janar din soja

"Mun nesanta kanmu baki daya daga abin da ya aikata sannan kuma mun yi alkawarin daukar matakin da ya dace.

"Kazalika mun bukaci faston da ya ajiye duk wani mukami da yake rike da shi a wannan coci mai albarka."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel