Kaura vs M.A: An karfafa tsaro a garin Bauchi yayinda kotu ke zaman raba gardamar zaben gwamna

Kaura vs M.A: An karfafa tsaro a garin Bauchi yayinda kotu ke zaman raba gardamar zaben gwamna

An karfafa tsaro a ciki da wajen kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi yayinda Alkalan kotun ke zaman raba gardama tsakanin gwamnan jihar, Bala Mohammad na jam'iyyar PDP da Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC.

Jami'an tsaro wadansa suka hada da yan sanda, jami'an NSCDC, jami'an DSS da wasu na leken asiri sun mamaye titin Ahmadu Bello way da titin Yandoka da safiyar nan. Punch ta ruwaito.

An kulle hanyar gaba daya kuma an umurci mutane su bi wasu hanyoyin daban.

Hakan ya kawo matsala ga masu motoci haya, yan kasuwa da ofishohin ma'aikatan gwamnati da aka kulle.

A kotun kuma, jami'an tsaro sun hana mutane shiga har da yan jarida.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin yan tauri 1000 domin yakan Boko Haram

Tsohon gwamnan jihar Bauchi ya ci alwashin kai karar gwamnatin Jihar Bauchi zuwa kotu bisa rahoton da wani kwamitin gwamnatin ya fitar me cewa ana zarginsa da baddakalar wadansu kudade.

A cikin wani zance da ya samu sanya hannun hadimin tsohon gwamnan, Ali M. Ali jiya Asabar 5 ga watan Oktoba a Bauchi ya ce, tsohon gwamnan zai dauki matakin shari’a a kan kazafin da akayi masa na cewa ya wawure wasu kudade.

Kwamitin bincike da kuma dawo da kudaden gwamnatin da ake sace na Bauchi ne ya fitar da wani jawabi ranar Laraba 3 ga watan Oktoba inda ya ayyana gwamna Abubakar da cewa yak eta dokokin kula da wasu kudade mallakar gwamnatin jihar Bauchi a lokacin mulkinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel