Gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin yan tauri 1000 domin yakan Boko Haram

Gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin yan tauri 1000 domin yakan Boko Haram

Gwamnatin jihar Borno ya kaddamar da sabuwar hanyar fito na fito da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram da suka addabi sassan jihar da yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya dauki yan tauri 1000 a boye daga sassan Najeriya musamman Arewa maso gabas da yamma.

Rahotannin sun bayyana cewa wadannan yan tauri ba su jin harbin bindiga kuma suna iya bacewa.

Zulum wanda farfesa na a sashen injiniyanci ya bayyana tashin hankalinsa kan sabuntar rikicin Boko Haram a jihar duk da namijin kokarin da Sojoji keyi.

A makon da ya gabata, hukumar sojin Najeriya ta shirya taro domin tattaunawa kan yadda za'a fara gudanar da addu'o'i kan yan ta'adda.

A ranar Juma'a, gwamna Zulum ya dauki masallata 30 domin gudanar da ibadah a masallacin Ka'abah kan yan Boko Haram.

KU KARANTA: Tashin hankali: Ba zan sauko ba sai Buhari ya yi murabus - Matashi ya hau falwayan Glo

Majiyar tace: "An dauki wadannan yan tauri na musamman daga yankin Arewa maso gabas da yamma. Wasu yardaddun hadimai ne gwamna Zulum ya ba wannan aiki."

"Wannan shine karo na farko da za'a yi amfani mutane daga wajen yankin. Ana kawosu Borno cikin dare saboda gudun idanuwan jama'a."

The Cable ta samu rahoton cewa a kaddamar da daukan yan taurin ne a makonni biyu da suka gabata inda aka sanyasu rantsuwa da Alkur'ani mai girma.

Hakazalika an basu bindigogi, adduna da dukkan abubuwan da suka bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel