Na umurci dukkan ma'aikatan bangaren ilimin jihar Kaduna su sanya yaransu a makarantan gwamnati - El-Rufa'i

Na umurci dukkan ma'aikatan bangaren ilimin jihar Kaduna su sanya yaransu a makarantan gwamnati - El-Rufa'i

Kamar yadda yayi alkawari a shekaru biyu da suka gabata, gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i, ya shigar da yaronsa, Abubakar Al-Siddique El Rufa'i, makarantar gwamnatin Kaduna Capital School dake unguwar Malali Kaduna.

A ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, Gwamnan tare da amaryarsa sun kai Abubakar mai shekaru 6 da haihuwa makarantar inda zai yi karatun firamarensa.

Makonni biyu bayan kai yaronsa, gwamna Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ya laburtawa dukkan ma'aikatan bangaren ilimin jihar Kaduna cewa ya zama wajibi su kai yaransu makarantun gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Dalilin da yasa muke rusa gidajen karuwai da mashaya - Gwamnatin jihar Borno

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a fadar shugaban kasa Abuja inda yace:

"Mun bada umurninn cewa ya zama wajibi dukkan ma'aikatan ma'aikatar ilmin jihar Kaduna da ke da hakkin inganta ilimin yaranmu su sanya yaransu a makarantar gwamnati."

"A kan al'amarin kai yarona makarantan gwamnati kuma, wannan alkawari ne na cika kuma hakan ya bayyana cewa na yi imani da ingancin makarantun gwamnati tun da yarona na zuwa."

Hakazalika Gwamna Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ba zai cire yaronsa, Abubakar El-Rufa'i, daga makarantar gwamnati ba duk da garkuwa da mutanen da akayi da daliban wata makaranta a jihar jiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel