Tsohon Farai Ministan Ingila ya fadi dalilin da yasa Jonathan ya hana a ceto 'yan matan Chibok

Tsohon Farai Ministan Ingila ya fadi dalilin da yasa Jonathan ya hana a ceto 'yan matan Chibok

Tsohon Farai Ministan Ingila, David Cameron ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya hana su ceto 'yan matan da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace daga makarantar sakandire na Chibok a jihar Borno.

Acewar Cameron, Jonathan ya hana sojojin Birtaniya damar ceto 'yan matan saboda yana ganin lamarin kawai siyasa ce da aka shirya don bata masa suna.

A littafin da ya wallafa cikin 'yan kwanakin nan, mai taken 'For the Record', Cameron wadda ke kan mulki lokacin da aka sace 'yan matan ya ce sojojin Birtaniya sun gano inda wasu daga cikin wadanda aka sace suke kuma sun nemi a basu izini su taimaka ammma Jonathan bai amince ba a cewar The Cable.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Cameron ya rubuta, "A farkon 2014, wasu mayaka sun shiga makarantar sakandire ta gwamnati da ke kauyen Chibok inda suka sace 'yan mata kanana 276.

"An tafi da su wani sansani cikin kurmin daji. An tilastawa kiristoci daga cikinsu su musulunta. An sayar da wasu cikinsu a matsayin bayi inda suka fuskanci fitina kamar yadda matan Yazidi suka fuskanta.

"Bayan kamfen din Bring Back Our Girls ya watsu a duniya, mun hada gwiwa da sojoji da kwararrun jami'an bincike sirri a Najeriya kuma muka aike da jiragen leken asiri da wasu na'uarori na musamman domin neman 'yan matan. Duk da girman dajin ya rubanya girman Wales sau uku, mun gano inda wasu daga cikinsu su ke.

"Amma shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan kamar bai damu ba. Daga baya da ya yi jawabi kan batun sai ya yi ikirarin cewa masu neman a ceto yaran suna yi ne don dalilan siyasa. Da muka nemi izinin mu ceto 'yan matan da muka gano, bai bamu izini ba."

Sai dai a bangarensa Shugaba Goodluck Jonathan ya karyata batun na Cameron. Ya yi ikirarin cewa Cameron ya masa sharri ne saboda yana fushi da shi domin ya ki amincewa da halasta yin auren jinsi guda a yayin da ya ke shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel