Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya

- Fatan kowa a rayuwa ya girma sannan ya samu madafa a rayuwa

- Akan fara wannan kokarin ne tun ana yara, wasu yaran kan nasibi tun suna kanana, wasu kuwa kan samu tun suna yara

- Kananan yara ne da suka tara miliyoyin nairori sakamakon baiwar da suka mallaka kuma suke bayyanata

Lokacin muna yara, fatanmu watarana mu girma kuma mu samu abin hannu. Duk da dai baiwa bata san shekaru ba matukar kana da burin bayyanata a duniya.

Hakan ce kuwa ta kasance da wasu yara sanannu a Najeriya wadanda suka samu hanyar cin abinci a masana'antar nishadantarwa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe sojoji 9 a jihar Zamfara

1. Emmanuella

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

Cikakken sunanta shi ne Emmanuella Samuel. An haifeta a ranar 22 ga watan Yuli, 2010. Yarinya ce da ke nishadantarwa da gajerun bidiyoyinta a kafar YouTube. Ta fara sana'ar nishadantarwa ne tun tana da shekaru 5 a duniya.

Ta karbi kyautuka da dama akan kananan bidiyoyinta. A halin yanzu yarinyar na da dukiyar da ta kai $90,000 wacce ta wuce naira miliyan 20.

2. Ahmed Star Boy

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

Kafin haduwar yaron da shahararren mawaki Wizkid, Ahmed yaro ne mai fatan zama tauraro a masana'antar waka.

A 2017, yaron ya samu sa'ar haduwa da mawaki Wizkid a wani wasa da yaje inda ya hango yaro karami cikin mutane ya dage yana rera wakarsa ta "Why you never sleep, come on stage."

Yaron ya yi amfani da damarsa ne a take inda ya rero wasu baitukan gambara wadanda suka saka mawakin siyansa don shiga cikin kungiyarsa a naira miliyan 10.

A halin yanzu arzikin Ahmed ya kai naira miliyan 10.

3. Destiny Boy

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

Afeez Adesina wanda aka fi sani da Destiny Boy ya zama sananne ne bayan da ya fito a wakar IF ta Davido.

Baiwarsa da kokarinsa yasa ya shahara a masana'antar waka ta Najeriya.

An haifi yaron mai shekaru 15 a Agege. Kamar yadda yace, yanayin tsarin wakarsa ya samo asali ne daga inda ya girma. Yana da dukiya kusan naira miliyan 8.

4. DJ Young Money

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

Yana daya cikin yara sanannu masu kudi a Najeriya. Hazikin yaron mai shekaru 12 ya samu miliyoyin nairori ne bayan kwangiloli kala-kala da yayi.

A 2016, ya sa hannu da kamfanin nishadantarwa na K-Nation a matsayin mai kida. Ya gaji wannan aiki ne daga mahaifinsa.

Dukiyarsa ta kai akalla naira miliyan 20.

5. Egypt Ify Ufele

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

Ify 'yar Najeriya ce kuma da America. Ta kware wajen hada kaya na kowanne sha'ani.

Itace ta kirkiro Bully Chasers Charity. An ruwaito cewa ta fara sana'ar kayan sawa ne bayan da aka zalinceta a makaranta.

Karamar yarinyar mai shekaru 14 an haifeta ne a ranar 3 ga watan Mayu, 2005.

Yayarta Sade Perry madinkiya ce. Hakan kuwa na daga cikin abinda ya ja ra'ayinta ta fara dinki. A shekarunta, tana da dukiya akalla naira miliyan 10.

6. OzzyBosco Wonderkid

Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Sanannun yara 6 masu hannu da shuni a Najeriya
Asali: Twitter

An haifeshi a ranar 7 ga watan Janairu, 2007 a Najeriya.

A shirinsa na farko da ya bayyana a gidan talabijin, an fara danganta shi da D'Banj da kuma Naeto C. Ya kokarta sosai wajen yin suna a nahiyar Afirka.

Yana da dukiyar da ta kai naira miliyan 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel