Da arziki a gidan wasu: An binciko wani tsohon gwamna da ya siyarwa kansa motocin gwamnati a rahusa

Da arziki a gidan wasu: An binciko wani tsohon gwamna da ya siyarwa kansa motocin gwamnati a rahusa

- Kwamitin bincike da dawo da kadarori da kudaden jihar Bauchi ya gano cewa tsohon gwamnan jihar ya siyarwa kansa motocin alfarma

- Tsohon gwamnan jihar Bauchin ya siyarwa kansa motocin ne cikin arha da rahusa

- Tsohon mai bada shawara ga tsohon gwamnan jihar ya kare abinda ubangidan nasa ya yi

Kwamitin dawo da kadarorin jihar Bauchi ta zargi tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abubakar, da siyarwa kansa motoci bakwai na alfarma a N19,877,275 kafin ya sauka kujerar shugabancin jihar.

A ranar 12 ga watan Yuli, 2019 ne gwamnan jihar, Bala Mohammed ya tilasta binciko duk kudade da kadarorin gwamnati da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi awon gaba da su.

KU KARANTA: Sabon salo: An gyara titin wata jiha da kankare a maimakon kwalta

Jami'in hulda da jama'a na kwamitin, Alhaji Umar Ningi ya sanar da manema labarai cewa, kwamitin na aiki ne da dokokin tarayya da sauran dokokin majalisar jihar.

Ningi ya zargi cewa, daya daga cikin motocin alfarmar da tsohon gwamnan ya siyarwa da kansa akwai wata mota ta naira miliyan 150 wacce ya siyarwa kansa a naira miliyan 7.8.

"Motar ana samunta a naira miliyan 150 amma tsohon gwamnan ya siyarwa kansa a naira miliyan bakwai da dubu dari takwas," in ji shi.

Ya ce hakan yaci karo da tanadin kasafin kudi da dokokin siyan kayan gwamnati na jihar Bauchi.

Ya ce, "Sauran motocin da ya siyarwa kansa sun hada da mota kirar Landcruiser V8, Toyota Hilux guda biyu, Range Rover SUV har uku."

Ningi ya kara da cewa, jami'an tsohuwar gwamnatin sun yi awon gaba da motocin alfarma har 30 kafin su bar ofishinsu amma a halin yanzu an samo 15 inda ake cigaba da neman sauran 15 din.

Kamar yadda Ningi ya sanar, kwamitin ta gano cewa tsohon gwamnan ya siyarwa kansa gidan gwamnatin jihar da ke gefen otal din Wikki a kudi kalilan.

A maganar da manema labarai suka yi da tsohon mai bada shawara ga tsohon gwamnan, Ali M. Ali ya kare abinda ubangidansa ya yi.

Yace shari'a ta amince jami'in gwamnati ya siya abun hawan gwamnati matukar an shekara uku ana amfani da shi.

Ali ya ce, "Hankalinmu ya kai kan maganganu akan 'zunuban' tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, lokacin yana kan kujerarsa."

Ya cigaba: "Dokar gwamnati itace in dai aka yi amfani da abun hawa mallakin gwamnati na shekaru uku, za a iya siyansa. Ababen hawan da ke magana kuwa anyi shekaru hudu ana amfani dasu. Dokar kuma ta ce za a iya siyarda abun hawan a kashi goma na asalin kudinsa."

"Maganar gaskiya, motoci kirar Hilux din na tawagar tsohon gwamnan na da matsalar inji ne." In ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel