Yanzu-yanzu: FG ta dakatar da daukan sabbin ma'aikata a NDDC

Yanzu-yanzu: FG ta dakatar da daukan sabbin ma'aikata a NDDC

Gwamnatin Tarayya ba bayar da umurnin dakatar da daukan ma'aikata a hukumar cigaban yankin Neja Delta nan take kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayar da umurnin inda ya kuma ce a dakatar da bayar da takardan daukan aiki da sauran harkoki da suka shafi daukan aiki a cibiyar ta NDDC.

Sanawar ta babban sakataren yadda labaran ministan, Anietie Ekong ta fitar ranar Asabar ya ce Akpabio ya bayar da umurnin ne cikin wata wasika da sakataren dindindin na ma'aikatan Neja Delta, Didi Walson-Jack ya aike wa mukadashin direktan NDDC, Dakta Akwagaga Enyia.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

Ya ce, "A cewar umurnin da ministan ya bayar, hukumar ba ta da kudin daukan sabbin ma'aikata saboda haka ta koma yadda ta ke gudanar da lamarun ta kamar ranar 31 ga watan Augusta yayin da ya umurci a bashi rahoton dukkan wadanda aka dauka aiki.

"Wasikar ta ce an dakatar da daukan aikin ne har sai an gudanar da bincike na kwafkwaf kan daukan aikin da akeyi sannan kwamitocin NDDC na majalisar dattawa su san matakin da za su dauka a kan mukadashin shugaban na NDDC."

Majiyar Legit.ng a ranar Laraba ta ruwaito cewa a ganawar farko da Akpabio ya yi da mahukunta cibiyar ta NDDC karkashin jagorancin Enyia a ranar 4 ga watan Satumba ya shaida musu cewa abubuwa za su canja a hukumar kuma zole su zage damtse.

Ministan ya ce za a gudanar da binciken kwafkwaf kan dukkan kudaden da suka shigo ma'aikatar da aka kiyasta sama da tiriliyan 2 domin gano yadda aka kashe kudaden.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel