Borno: Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 3 a Gwoza, sun kwato makamai

Borno: Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 3 a Gwoza, sun kwato makamai

Dakarun sojojin Najeriya tare da hadin gwiwan 'yan sa-kai sunyi nasarar datse 'yan wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne a mahadar Banki Road da ke Pulka a Gwoza a Borno inda suka kashe uku cikinsu a daren ranar Alhamis.

Mataimakin direktan yada labarai na sojojin, Kwanel Ado Isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Isa ya ce an yi nasarar kai sumamen ne sakamakon bayyanai masu amfani da wasu 'yan kasa na gari suka bawa sojojin game da 'yan ta'addan a Pulka da ke Gwoza.

Ya ce wasu adadin 'yan ta'addan da ba a tabbatar ba sun jikkata yayin artabun inda ya kara da cewa babu wani wanda ya rasu a bangaren sojojin da 'yan sa-kai.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

A cewarsa, an kwato bindigu kirar AK 47 biyu da kekunan hawa biyu daga hannun 'yan ta'addan.

Ya ce, "Kazalika, misalin karfe 10:50 na daren Alhamis a wata abu mai kama da harin ramuwar gayya kan kisar 'yan ta'ddan da sojoji su ka yi, wasu miyagu sun kai wa sojojin Delta Company hari a SRA da ke Pulka.

"Sojojin sun dakile harin cikin gaggawa inda suka kashe 'dan bindiga guda daya kuma suka kwato AK 47 guda daya.

"Babu wanda ya mutu a bangaren sojojin da 'yan sa-kai.

"Mukadashin kwamandan GOC 7 kuma kwamandan sector 1 na Operation Lafiya Dole Brig Janar A.K. Ibrahim ya ziyarci SRA Pulka inda ya gana da sojojin.

"Ya yaba musu kan nasarorin da suka samu kawo yanzu kuma ya bukaci kada suyi kasa a gwiwa a kokarin su na kawo karshen ta'addanci a yankin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel