Shugaba Halimah na cikin musulmi 50 da suka fi kowa karfin fada a ji a duniya

Shugaba Halimah na cikin musulmi 50 da suka fi kowa karfin fada a ji a duniya

Shugaba Halimah Yacob ta samu shiga cikin jerin mutane 50 na farko a jerin sunayen musulmi 500 da suka fi kowa karfin fada aji a duniya kamar yadda cibiyar Royal Islamic Strategic Centre da ke kasar Jordan ta wallafa.

An zabi Uwargida Halimah a matsayin shugaban kasar Singapore mace na farko a shekarar 2017 kuma ita ce kadai 'yar kasar Singapore kuma daya cikin mutane da biyar da Kudu maso gabashin Asia a cikin jerin mutane 50 a jerin sunayen masu fada aji na shekarar 2020.

Ita kadai ne kuma mace a jerin mutane 50 na farko kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan shine karo na 11 da cibiyar ke wallafa sunayen musulmi a duniya bisa la'akari da irin gudunmawar da suka bawa al'ummarsu.

DUBA WANNAN: Gwamnan PDP ya umarci a mayar da sunan Sardauna a titin da aka sauya da sunansa

An zabi Uwargida Halimah ne saboda kokarin da ta keyi na inganta hadin kai da kwato hakkin ma'aikata.

Daya daga cikin tsare-tsaren da ta fito da su a matsayinta na shugaban kasa sun hada da kiran taro na musamman na shugabanin addinai daban-daban domin inganta fahimtar juna tsakaninsu.

Wannan taron ya zama taro na kasa da kasa karo na farko da aka gudanar a wannan shekarar inda shugabanin addinai suka hadu domin tattaunawa.

Ta kuma bullo da sabon shiri na musamman domin nuna godiya ga ma'aikata da ba a cika ganin fuskokinsu a kafafen yada labarai ba kamar direbobi da sauransu.

Sauran mutanen da suka samu shiga jikin jerin mutane 50 masu fada aji a duniya daga yankin Kudu maso gabashin Asia sun hada da shugaban kasar Indonesia Joko Widodo (13), Farfesa KH Said Aqil Siradj, shugaban Nahdlatul Ulama na Indonesia (19), da mai wa'azi na kasar Indonesia Habib Luthfi Yahya (33) da Faraiministan Malaysia Mahathir Mohamad (42).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel