Magidanci ya bankawa matarsa wuta

Magidanci ya bankawa matarsa wuta

- A ranar asabar da ta gabata ne wani magidanci ya bankawa matarsa wuta a yankin Nakuru County da ke kasar Kenya

- Mijin ya zargi matarsa da kin dawowa gida da wuri ne bayan tafiyar da tayi zuwa Nairobi a ranar juma'a

- Ya watsa mata fetur ya rufe ta cikin gida bayan da ya kyasta mata ashana

Jami'an tsaro sun kama wani magidanci a kasar akan laifin bankawa matarsa wuta saboda bata dawo gida da wuri ba.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa, Lucy Nyira mai shekaru 25 na zama da munanan raunika a aibitin Nakuru da ke jihar bayan da mummunan abin ya faru.

Mijinta Bernard Kariha mai shekaru 24 ya banka mata wuta inda ya kone kusan kashi daya bisa hudu na jikin matarsa.

KU KARANTA: Mace mai kamar maza: Ta adana kwalin digirinta, ta tsunduma tukin Keke Napep

Lamarin ya auku ne a daren asabar, 28 ga watan Satumba a kauyen Kiratina a Nakuru, kasar Kenya.

Lucy ta tafi Nairobi a ranar Juma'a don saro kayan siyarwanta inda ta dawo washegari.

Lokacin da musu ya barke tsakaninta da mijinta, kawai sai ya watsa mata fetur inda ya kyasta wuta tare da rufe ta cikin gida don ta mutu.

Kashi daya bisa hudu na jikin Lucy ya kone lokacin da makwafta suka kai mata dauki. A take suka garzaya da ita asibiti inda likitoci suka rufa akanta don ceto ratuwarta.

Kamar yadda gidan talabijin na Citizen ya bada rahoto, dama tuntuni Bernard ya saba da musgunawa matarsa tare da kyara.

Shugaban 'yan sandan Nakuru County, Stephen Matu ya tabbatar da cewa wanda ake zargin na hannunsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel