Mace mai kamar maza: Ta adana kwalin digirinta, ta tsunduma tukin Keke Napep

Mace mai kamar maza: Ta adana kwalin digirinta, ta tsunduma tukin Keke Napep

- A ranar Alhamis ne kamfanin dillancin labarai ya tattauna da mata masu sana'ar tukin Keke Napep a garin Legas

- Daya daga cikinsu ta bayyana cewa, ta adana kwalin digirinta ne yayin da aiki yaki samuwa. A ddon haka ne ta fada sana'ar sufurin

- Wata mahaifiyar yara 3 ta sanar da cewa, maigidanta ne ya bata kwarin guiwar sana'arta inda har ya siya mata Keken da kudinsa

A ranar Alhamis, matan da suka tsunduma a harkar tuka Keke Napep a garin Legas sun nuna farincikinsu gani da cewa suna morar kasuwancin da aka fi sanin maza dashi.

Wasu daga cikin matan da suka fada harkar tuka babur din sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai a Legas irin gogewar rayuwa da suke samu.

Alabi Latifat, matukiyar keke Napep ce da ke aiki a yankin Mushin da Yaba a jihar Legas.

Ta sanar da kamfanin dillancin labarai yadda ta yanke shawarar tsunduma harkar tuka keken bayan da ta gagara samun aikin yi da kwalin babbar dufulomarta.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama makasa masu amfani da kayan sojoji

Latifat ta ce, ta shiga jerin masu sana'ar safurin ne a 2017 kuma ta fuskanci kalubale da dama a rayuwarta, wanda a halin yanzu ya zama tarihi.

"Ina da ilimi amma lokacin da aikin yi yaki zuwa, sai kawata da ke harkar tuka keke ta shawarceni da in fara nima. Abinda har yau kuwa banyi danasani ba."

"Bayan a kalla a wuni daya ina hada 5000, mutane suna daraja ni tare da girmama ne akan titi," in ji ta.

Hakazalika Celestina Iredia mai tuki a yankin Abule Egba na jihar Legas, ta ce, ta samu kwarin guiwar fara sana'ar ne daga mijinta bayan da ya siya mata keke Napep din.

Iredia mai yara 3, ta ce ta fara saide-saide amma babu ribar da zata sa ta tallafi mijinta don kula da iyali.

"Kwarin guiwa daga mijina shi ne ginshikin aikin nan nawa. Haka kuma taimakon da nakan yi a cikin gidana yasa matsalolin rayuwa suka rage mana." In ji ta.

Wata matukiyar, Kikelomo Hassan da ke aiki a yankin Agbado Crossing zuwa Dalemo a jihar Legas ta sanar da kamfanin dillancin labarai cewa, tana farincikin kwarin guiwar da yabon da take samu daga fasinjoji.

Ta ce mutane da yawa sun fi son hawa Kekenta saboda sun yarda cewa a matsayinta na mace zata tukasu a hankali da kuma lura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel