Yadda wani mutum ya yi kokarin kashe tsohuwar matarsa da bam

Yadda wani mutum ya yi kokarin kashe tsohuwar matarsa da bam

Wani mutum mai shekaru 28 ya yi yunkurin halaka tsohuwar matarsa da bam din da ake kera wa a gida wadda ya fashe a fuskarta kamar yadda 'yan sandan kasar Austria suka ce a ranar Alhamis.

Bam din ya yi wa matar mai shekaru 27 da yara 3 munanan rauni hakan yasa aka kwantar da ita a wani asibiti da ke Kudancin Austria bayan harin na ranar Talata.

Tuni dai an yi mata tiyata biyu sannan ta yi munanan kuna a kashi 40 cikin 100 na sassan jikinta.

Bam din ya fashe ne bayan da ta fita kofar gidan ta da ke Guttaring a jihar Carinthia ta dauki wani kwali da aka ajiye mata.

'Yan sandan garin, a ranar Alhamis sun sanar da cewa sun kama tsohon mijinta da wani wanda ya taimaka masa da suka amsa laifin yunkurin kisan kai.

DUBA WANNAN: Mota dauke da fasinjoji ta tsinduma cikin rafi, mutum 10 sun mutu

Wanda ya taimaka masa, tsohon soja ne ya kai bam din kofar gidan matar a cikin kwali sannan ya kwankwasa kofa ya kuma tsere.

Tsohon mijinta wadda shima tsohon soja ne shi kuma yana labe bayan wasu ciyayi kusa da gidan inda ya kuna bam din a cewar sanarwar da 'yan sanda suka bayar.

An kama tsohon mijin a ranar da abin ya faru yayin da shi kuma wanda ya taimaka masa aka kama shi a ranar Alhamis.

'Yan sanda sun ce mutane biyun sunyi gwajin bam din a cikin daji bayan sayan kayan bam din a intanet.

Alkallumar da ma'aikatar cikin gida na Austria ta fitar ya nuna cewa cikin mutane 73 da aka kaiwa hari gidajensu 41 mata ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel