Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)

Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)

A yayin da jama'a ke rungumar tsarin takaita haihuwa, musamman a kasashe masu yawan jama'a, wani mutum a kasar Indiya ya haifi 'ya'ya 94 tare da matansa 39.

Mutumin mai suna Ziona China ya zama magidanci mafi yawan iyali a duniya.

Ziona, shugaban wata mazahabar addinin Kirista "Chana" na zaune tare da iyalinsa a wani katafaren gida mai dakin kwana 100 da ke garin Baktwang a kasar India.

Dukkan iyalinsa na zaune tare da shi a gida daya. Matansa na yin rukuni tare da yin karba-karba ta dafuwar abinci, 'ya'ya mata kuma su tsaftace gida yayin da 'ya'ya maza ke fita kwadago domin nemo abinci.

Wani abu da ya bawa jama'a mamaki shine yadda iyalin suka rike da kansu ba tare da fuskantar tsananin kuncin rayuwa ba, don kuwa basa bara duk da idan an basu gudunmawa suna karba.

DUBA WANNAN: A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7

Idan dare ya yi, Ziona na kasancewa tare da dukkan matansa 39 ta hanyar kewaya wa zuwa dakunansu.

Duk da yana da mata 39, Ziona ya ce basu ishe shi ba, tare da bayyana cewa yana neman kari.

"Akwai mutane da yawa a karkashin kulawa ta, ina ganin kai na a matsayin mutum mai sa'a", a cewarsa.

Huntharnghanki, daya daga cikin matan Ziona, ta ce suna zaune lafiya da juna, ba tare da nuna kishi a tsakaninsu ba.

Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)
Gidan da Zion ke zaune da iyalinsa
Asali: Twitter

Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)
'Ya'yan Zion na cin abinci
Asali: Twitter

Ayu: Mutum daya ya auri mata 39, ya haifi 'ya'ya 94 (Hotuna)
Zion da matansa 39
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel