Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun dira makaranta a Kaduna, sun yi awon gaba da dalibai mata

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun dira makaranta a Kaduna, sun yi awon gaba da dalibai mata

Wasu yan bindiga sun fasa makarantar sakandare a jihar Kaduna cikin dare inda sukayi garkuwa da dalibai mata shida da malamai biyu. Premium Times ta bada rahoto.

Yan bindigan sun dira kwalegin Engravers dake unguwar Sabo, karamar hukumar Chikun misalin karfe 12:10 na dare, ma'ajin makarantan Elvis Allah-Yaro ya bayyanawa manema labarai.

Wata mahaifya ta bayyana cewa akwai yaranta biyu cikin wadanda aka sace.

Yace: "Jami'an tsaro sun fara kaddamar da bincike kuma sun bazama suna neman yan matan da malamai biyu a aka sace."

Ya kara da cewa kwamishanan harkokin tsaron cikin Kaduna, Samuel Aruwan, ya hallara a makarantan kuma yana baiwa jami'an tsaro goyon baya.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Abubakar Sabo, bai yi tsokaci akan lamarin ba.

KU KARANTA: Mutane 6 da Allah ke karban addu'ansu a koda yaushe

Wannan abu ya faru yayinda sassan jihar Kaduna ke fama da hare-hare daga masu garkuwa da mutane.

A shekarar 2019 kadai, an yi garkuwa da daruruwan mutane a jihar Kaduna musamman a kan titin Kaduna zuwa Abuja.

A yanzu mutane sun kauracewa hanyar yayinda manyan jami'an tsaro suka koma bin jirgin kasa.

A bangare guda, Hukumar yan sandan jihar Gombe ta damke wani matashi dan shekara 19, Mohammed Sani Adamu, mazaunin Gabukka quaters kan zargin garkuwa da wani yaro mai shekaru 7 da haihuwa.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Obed Maru Malum, ta bayyanawa manema labarai cewa jami'an SARS sun damke matashin ne a ranar 23 ga Satumba, kwanaki uku bayan ya sace yaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel