Mutane 6 da Allah ke karban addu'ansu a koda yaushe

Mutane 6 da Allah ke karban addu'ansu a koda yaushe

A cikin tabbatattun hadisai kuma sahihai, akwai wasu mutane shida da Allah ke karban addu'o'insu a duk lokacin da suka gabatar.

Hadisi ya tabbata daga manzon Allah (SAW) cewa dukkan addu'ar da musulmi yayi, Allah na karba amma ta hanyoyi uku; cikin Allah ya karba kuma dan Adam ya gani, ko Allah ya yi amfani da addu'an wajen kawar masa da wani bala'i da zai fado masa ko kuma a ajiye masa har lokacin da ya gamu da Allah.

A yau mun kawo muku mutane shida da Allah ke karban addu'o'insu:

1. Addu'ar mara lafiya

Hadisi daga Umar bin Khattab inda yace: "Manzon Allah (ﷺ) ya ce: 'Idan ka ziyarci mara lafiya, ka bukaceshi yayi maka addu'a, saboda addua'rsa kaman na mala'iku ne." (Sunan Abi Dawud).

2. Addu'ar mai azumi

Mai azumi na da wani lokaci mai muhimmanci da ake karbar addu'arsa. Wannan lokaci wasu yan mintuna ne kafin shan ruwa.

Hadisi daga Abdullahi bin Amr bin Aas ya ce manzon Allah ﷺ ya ce: "A lokacin da mai azumi ya sha ruwa, ba za'a mayar da addu'o'insa ba." (Sunan Ibn Majah, babi na 7, hadisi 1825)

3.Addu'an mahaifi ga yaransa

Iyaye mata suna yiwa yaransu addu'a koda yaushe amma iyaye maza sukan shagala da yiwa yaransu addu'a.

Abu Hurairah ya ruwaito Hadisi daga manzon Allah ﷺ cewa : "Akwai addu'o'i uku da ake karba, ko shakka babu: Addu'an wanda aka zalunta, addu'an matafiyi da add'uan mahaifi ga 'dansa." (Jami'at at-Tirmidhi 1905)

4. Addu'an Musulmi ga dan'uwans a bayansa

Addu'an Musulmi ga dan'uwansa Musulmi a bayan idonsa na da matukar muhimmanci ga shi da dan'uwan nasa.

Ummu Dardaa ta ruwaito hadidi cewa: Mijina ya ruwaito cewa ya ji manzon Allah ﷺ yana cewa: "Duk wanda ya yiwa dan'uwansa addu'a a bayan idonsa, mala'ika zai ce 'Amin, kaima haka." (Muslim 2732)

5. Addu'an Matafiyi

Manzon Allah ya ce tafiya wani yanki ne na azaba, shi yasa aka bada daman ajiye azumin farilla idan musulmi na kan hanya

Abu Hurairah ya ruwaito Hadisi daga manzon Allah ﷺ cewa : "Akwai addu'o'i uku da ake karba, ko shakka babu: Addu'an wanda aka zalunta, addu'an matafiyi da add'uan mahaifi ga 'dansa." (Jami'at at-Tirmidhi 1905)

6. Addu'an wanda aka zalunta

Abu Hurairah ya ruwaito Hadisi daga manzon Allah ﷺ cewa : "Akwai addu'o'i uku da ake karba, ko shakka babu: Addu'an wanda aka zalunta, addu'an matafiyi da add'uan mahaifi ga 'dansa." (Jami'at at-Tirmidhi 1905)

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng