Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: An halaka wani jagoran Fulani a Adamawa

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: An halaka wani jagoran Fulani a Adamawa

Yan bindiga sun kashe wani shahararren shugaban Fulani a yankin karamar hukumar Yola ta Kudu da ke jihar Adamawa.

An harbi Alhaji Abdu Bali, Shugaban kungiyar Fulani na Tabbital Pulaku Joondie Jam reshen jihar tare da wani bako a gidansa da misalin karfe 8:00 na daren ranar Talata.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da harin, cewa rundunar ta fara bincike a lamarin domin gano wadanda suka aikata ta’asar.

Gwamna Ahmadu Fintiri yayi Allah wadai da harin a Wani jawabi daga darakta janar na labaransa a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada sabon manajan darakta na NIWA

Jawabin ya kuma yi Allah wadai da kisan Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a unguwar Muchala dale karamar hukumar Mubi ta arewa, Ishaya Dauda, wanda ya afku a ranar Litinin. Ya Kara da cewa gwamnan ya bukaci yan sanda da su tsamo makasan shugabannin biyu domin fuskantar shari’a.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa 'Yan bindiga sun kashe dan majalisa, Venture Kagbude a karamar hukumar Sapele ta jihar Delta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ana zargin hayar 'yan bindigar hayarsu aka yi don kashe dan majalisar inda kuwa suka kashesa a ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, 2019 akan titin Warri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel