An bindige wani shugaban Fulani har lahira a Adamawa

An bindige wani shugaban Fulani har lahira a Adamawa

'Yan bindiga sun halaka wani fitaccen shugaban Fulani a karamar hukumar Yola ta Kudu na jihar Adamawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An harbe Alhaji Abdu Bali, shugaban kungiyar Tabbital Pulaku Joondie Jam, ne tare da wani da ya kawo masa ziyara a gidansa misalin karfe 8 na daren ranar Talata.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, Suleima Nguroje ya tabbatar da harin inda ya ce rundunar ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata mummunan ta'asar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe 'Iblis' a jihar Rivers

Gwamnan Jihar, Ahmadu Fintiri ya yi Allah wadai da harin cikin wata sanarwa da ya fitar da bakin Direktan yadda labarai na jihar a ranar Laraba.

"Gwamna Ahamdu Umaru Fintiri ya yi tir da kisar gillar da aka yi wa Alhaji Abdu Bali, shugaban Tabital Pulaku Joondie Jam da wani mutum daya a Yola," inji shi.

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da kashe shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na mazabar Muchala a karamar hukumar Mubi ta Arewa Ishaya Dauda da aka kashe a ranar Litinin.

Ta kara da cewa gwamnan ya bawa rundunar 'yan sandan umurnin binciko wadanda suka kashe shugabannin biyu domin a bi musu hakkinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel