Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari a ranar Talata ta taya 'yan Najeriya murnar cika shekaru 59 da samun 'yancin kai amma ba ta sanar da inda ta ke ba.

Wannan shine karo na farko da ta aike wa 'yan Najeriya sako bayan watanni biyu da ficewarta daga Najeriya.

Akwai masu hasashen cewa ta kauracewa fadar Aso Rock ne saboda wasu matsaloli na siyasa.

Duk da cewa ba ta fadi inda ta ke ba, tayi kira ga 'yan Najeriya masu hannu da shanu su kara kaimi wurin tallafawa rayuwar mata da yara a garurruwansu.

Aisha tayi wannan kirar ne a sakon ta na ranar bikin cika 'yancin Najeriya da ta wallafa a shafinta na Instagram da Facebook.

Ta ce, "A ranar bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kasar mu, Ina son in saka tabbatar da niyya ta na sawake rayuwar al'umma ta hanyar gidauniya ta na Aisha Buhari Foundation da wasu shirye-shiryen.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe 'Iblis' jihar Rivers

"Duk da haka, ina kira ga sauran 'yan Najeriya masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su kara kokarri a fanonin ilimi, lafiya, tallafawa al'umma da kare hakokin mata da yara. Nayi imanin al'ammura za su daidaita a gaba. Ina taya al'umma murnar ranar samun 'yancin kai na Najeriya."

Ana hasashen cewa Aisha ba ta samun yadda ta ke so a fadar shugaban kasar kuma ba ta gamsu da yadda wasu kusoshin fadar gwamnatin mai gidan ta ke tafiyar da wasu al'ammura ba.

Aisha ba ta kasar na tsawon watanni biyu tun bayan kammala aikin hajji. Ta tafi birnin Landan tare da mai gidanta bayan kammala aikin hajji a watan Augusta.

Amma direktan yada labarai na uwargidan shugaban kasar, Suleiman Haruna ya ce rashin ganin Aisha Buhari da ba a yiba na watanni biyu ba ta da alaka da wata dalili na siyasar fadar shugaban kasa.

Ya ce, "Kowa na da ikon walawa a duniya. Ita ba ma'aikaciyar gwamnatin Najeriya bane saboda haka bai kamata duk abinda tayi ya zama wani abin tattaunawa a kasa ba. Idan ta tafi kauyensu ko wani garin tayi watanni biyu mene zai sa ya zama wani abin tattaunawa a kasa?

"Ita 'yar Najeriya mai 'yanci kuma tana da ikon zuwa duk inda ta ke so."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel