Ke duniya: Matar uba ta kona 'yar kishiya akan 'rashin biyayya'

Ke duniya: Matar uba ta kona 'yar kishiya akan 'rashin biyayya'

- Hukumar NSCDC ta kama wata mata da ta kon diyar mijinta a jihar Barno

- Hauwa Adamu mai shekaru 38 ta kona gaban diyar mijinta mai shekaru 7 a duniya

- Majiya ta tabbatarwa da hukumar NSCDC din cewa kulawar yarinyar ta koma kan Hauwa ne bayan rabuwar mahaifiyar yarinyar da mahaifinta

Jami'an NSCDC na jihar Borno sun kama wata mata mai shekaru 38 a jihar da laifin kona diyar kishiyarta.

Hausa Adamu ta kona gaban diyar mijinta mai shekaru 7 a duniya.

Shugaban NSCDC, Abdullahi Ibrahim, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai a ranar Laraba a Maiduguri, cewa an kama matar ne a yankin Moduganari na jihar Maiduguri.

KU KARANTA: Mata 5 da suka fi kasaita a Najeriya

Ya ce, mutanen kirki ne daga yankin suka kawo musu rahoton aukuwar lamarin.

Ibrahim ya bayyana cewa, Hauwa ta yi hukuncin nan ga yarinyar ne bayan da ta zarge ta da rashin mata biyayya.

Kamar yadda ya sanar, binciken farko ya tabbatar da cewa, wacce ake zargin ta saba hantarar yarinyar.

Ibrahim ya ce, kular yarinyar ta koma hannun wacce ake zargin ne bayan rabuwar mahaifiyarta da mahaifinta.

Ya kara da cewa, an tura koken ga hukumar yaki da fataucin kananan yara ta kasa, wato NAPTIP don cigaba da bincike.

Wannan ba shi ne karo na farko da muka fara jin labarin mata masu gallazawa yaran miji ba saboda tsananin kishi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel