Jihar Akwa Ibom ta fi kowace jiha kwazo a Kudancin Kudu - Bankin Duniya

Jihar Akwa Ibom ta fi kowace jiha kwazo a Kudancin Kudu - Bankin Duniya

Bankin Duniya reshen kula da kaddamar da ayyukan ci gaba, ya bai wa jihar Akwa Ibom ta Najeriya lambar yabo a matsayin jihar da ta fi kowace jiha kwazo a bana a yankin Kudancin Kudu.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya reshen Afirka, Rachid Banmessaoud, shi ne ya ba da wannan sanarwa cikin wata rubutacciyar wasika ta lambar yabo da ya aike da ita zuwa gwmnatin jihar.

Bayan taya murna gami da farin ciki, Banmessoaud ya jinjina ga gwamnatin jihar Akwa Ibom dangane da yadda shugabannin Bankin Duniya suka yaba mata a sanadiyar kwazon aiwatar da muhimman ayyuka na ci gaba domin inganta jin dadin al'umma.

Ya kuma yaba wa kwazo da sadaukar da kai na gwamnatin Udom Emmanuel wanda a cewar ita ce ta ka muhimmiyar rawar gani wajen haskaka jihar da kuma kaita zuwa gaci na samun lambar yabo.

KARANTA KUMA: Najeriya na cikin hadari saboda sabawa yarjejiniya da ta kulla da wasu kamfanoni 11 a duniya

Legit.ng ta fahimci cewa, Bankin Duniya ya bai wa jihar Akwa Ibom wannan lambar girma a sanadiyar taka muhimmiyar rawar gani wajen aiwatar da muhimman ayyuka na na bunkasa ci gaba da kuma inganta jin dadin al'umma.

A wani rahoto mai nasaba da wannan, watanni kadan da suka gabata ne aka samu wani zakakurin yaro mai shekaru 15 a duniya, Hope Emmanuel Frank, wanda ya kera wata 'yar karamar motar hakar kasa wadda aka fi sani da tifa a jihar Akwa Ibom.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel