Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa shugaban al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa shugaban al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya rasuwa

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun: Allah ya yiwa mataimakin shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya kuma shugaban al'ummar Musulman Yarbawan Najeriya, Zakariyyau Babalola, rasuwa.

Imam Babalola ya kasance ajjajirin mai kudi kuma mai kyautatawa jama'a da dukiyarsa. Shine shugaban kamfanin Telemobile Nigeria Limited.

Shugaban, wanda ya kasance mataimakin sarkin Musulmin a NSCIA, ya mutu a jihar Legas yana mai shekaru 85.

Za'a gudanar da Sallar Jana'iza a babbar Masallacin jihar Legas dake Idumota misalin karfe 3 na rana.

Ana kyautata zaton babban limamin jihar Legas, Sulaimon Abou-Nolla, ne zai yi masa Sallah.

Shugaban kungiyar MMPN, AbdulRahman Balogun, ne ya tabbatar da wannan labarin ga manema labarai.

Yace: "Dr S.O . Babalola, shugaban al'umman Musulman Yarabawan Najeriya kuma mataimakin shugaban kasan NSCIA ya amsa kiran Allah da safen nan."

"Allah ya jikansa da rahman kuma ya azurtashi da al-janah Firdaus,”

"Za'a gudanar da Jana'izah misalin karfe 3:30 na yamma a masallacin Legas, Nnamdi Azikiwe Street, tsibirin Legas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel