Mata 5 da suka fi kasaita a Najeriya

Mata 5 da suka fi kasaita a Najeriya

- Najeriya ta kasance kasa mai albarkatu da dama, cikin kuwa har da mutanen da ke cikinta

- Akwai mata kasaitattu masu rinjaye da kasar ba a kasar kadai ba

- Matan sun taka rawar gani a siyasance, tattalin arziki da kuma zamantakewa

Ubangiji ya albarkaci kasar Najeriya da ni'imomi masu yawa. Ciki kuwa harda jajrtattun mata wadanda suka zama kalluba tsakanin rawuna.

Ba za a iya bada tarihin kasar ba, ba tare da an lissafo su ba sakamakon gudmmawar da suka bada a siyasa, zamantakewa da tattalin arziki na kasar. Ga kadan daga cikinsu.

Folunsa Alakija: Babbar 'yar kasuwa ce mai shekaru 68 a duniya. Ta gawurta ne a masana'antun kyale-kyale da man fetur. An lissafo Alakija a matsayin mace ta biyu mafi rinjaye bayan Ngozi Okonjo-Iweala. Ta zo a mace mafi rinjaye ta 80 a duniya a shekarar 2016 amma ta yo kasa a 2017 kamar yadda 'Forbes' ta bayyana.

Kamar yadda Forbes ta bayyana, dukiyarta ta kai $1.1bn.

Ngozi Okonjo-Iweala: Mace ce mai kamar maza. Ana matukar mutunta ta kuma tana daya daga cikin shuwagabanni mafi rinjaye na duniya. Masaniya ce a fannin tattalin arziki.

Tsohuwar ministar an haifeta ne a 13 ga watan Yuni na 1954. Kwararriyar masaniyar tattalin ce da habakarsa a duniya.

Dr Okonjo-Iweala ta karbai jinjina masu yawa a fadin duniya. Mace ce abar koyi ga matan duniya.

Ibukun Awosika: Tana daya daga cikin mata masu nasara a rayuwa. 'Yar kasuwa ce da ta zama kallabi tsakanin rawuna. Bata yarda cewa zamanta mace zai sa ta hakura ko ja baya daga wani kalubale ba.

Tana da ra'ayin dogaro da kanta. Hakan kuwa yasa ta kirkiro kamfanin kayan kawata daki mai suna 'Quebees' a 1989 wanda ya girma har ya koma Chair Centre Limited, daya daga cikin manyan kamfanonin kayan daki. Ibukun ta bada gudummawa mai matukar yawa wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

Wajen kawo gyara a bangarori canjin yanayi, lafiyar mata da habaka manyan gobe da sauransu.

KU KARANTA: Hukumar EFCC na kara tuhumar wani tsohon gwamna da wasu laifuka

Aisha Buhari: An haifi Aisha Muhammadu Buhari a ranar 17 Fabrairu 1971. Itace uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari. Masaniya ce a fannin gyaran fata kuma mahaifiyar yara biyar.

A shekaru da yawa, Aisha ta rike kasuwancinta cikin nasara. Ita ta kirkiro Hanzy Spa kuma shugabar tsangayar Hanzy Beauty da ke Kaduna da Abuja.

Aisha ta rufe shagon gyaran jiki da ta mallaka bayan da mijinta ya zama shugaban kasa. Mace ce abar kwaikwayo ga matan duniya. Mace ce mai rajin kare hakkokin mata da kananan yara. Tana kalubalantar auren yara mata da auren jinsi guda. Ta kasance jigo a yakin neman zaben mijinta a 2015.

Aisha mace ce mai nagarta wacce ta bada gudummawa ga habakar tattalin arzikin kasar nan.

Amina Mohammed: An haifeta a 27 ga watan Yuni, 1961 kuma a halin yanzu itace mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya.

Tsohuwar ministar muhallin a Najeriya itace ta biyu a iko a majalisar dinkin duniyar.

Amina ta kai matakin shuwagabannin duniya kuma tana kokari

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel