Harin Gubio: An kashe Sojoji 7, JTF 5, da yawa sun jikkata

Harin Gubio: An kashe Sojoji 7, JTF 5, da yawa sun jikkata

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu wanda ya hada da jami'an Sojoji bakwai yayinda da dama sun jikkata a mumunan harin da yan Boko Haram suka kai karamar hukumar Gubio ta jihar Borno a ranar Lahadi, 29 ga Satumba, 2019.

Rahoton ya bayyana cewa yan ta'addan sun kai harin ne matsugunnan Sojoji a Gubio inda aka yi artabu tsakaninsu da Soji.

A cewar majiya, yan ta'addan sun yi awon gaba da manyan makamai da motocin soji 6.

Yace: "Mun yi rashin mutane 12; Sojoji bakwai da dan sanda daya. Sauran biyar din mafarauta ne da yan kato da gora. Wadanda suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti domin jinya."

Wani dan banga ya bayyanawa manema labarai cewa sun yi rashin abokan aiki uku da dan kato da gora biyu da suke taimakawa Sojojin barikin Gubio.

Yace: "Yan Boko Haram sun shigo da yawansu suna harbin kan mai uwa da wabi. Hankalin jama'a ya tashi; mun yi kokarin dakilesu amma sun fi karfinmu."

A kwanaki bayan nan, garin Gubio ta fuskanci hare-haren Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel