Yan daba sun kashe uwa, sun jefa diyarta cikin rijiya a Kano

Yan daba sun kashe uwa, sun jefa diyarta cikin rijiya a Kano

Yan daba a unguwar Gobirawa yan yashi dake karamar hukumar Fagge ta jihar Kano sun kashe wata matar aure a cikin gidanta, sannan suka kashe diyarta kuma suka jefa gawarta cikin rijiya. Daily Trust ta bada rahoto.

Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa wannan abu ya faru ne tsakanin karfe 8 da 9 na daren Lahadi, 29 ga Satumba, 2019 kuma an kama mutane 6 da ake zargi.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da labarin ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ne ya jagoranci tawagar jami'an da suka damke su.

Ya ce an kwato muggan makaman da akayi amfani da su wajen aikata aika-aikan daga hannunsu.

Mijin marigayiyar, Malam Sha'abu Abdulmumini, ya tafi halartan waliman daurin aure a lokacin da abin ya faru da iyalinsa.

Yace: "Lokacin da na dawo misalin karfe 10 na dare, sai na kwankwasa kofa amma nayi mamakin rashin ganinta. Da farko na yi tunanin tana fushin dadewar da nayi ne har naga dai abin da gaske ne, sai na balle kofar na shige."

"Abin mamakin da na gani shine gawarta kwance cikin jini da diyarmu yar shekara 3 da muka gani cikin rijiya daga baya."

Hukumar yan sanda ta ce an kaddamar da binciken sirri bayan gurfanar da wadanda ake zargi a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel